‘Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’ar FRSC a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni daga Jos, Babban Birnin Filato, sun bayyana cewa wata jami’ar Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) mai suna Kate Jonathan Akpabio ta shiga hannun ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu dake jihar.

A wata sanarwa da mai sharhi kan harkar tsaro, Zagazola Makama ya wallafa ta kafar X, ranar Talata, ya ce lamarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:30 na safe, a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki gidanta dake yankin Rantya, inda suka tafi da ita.

Daga lokacin ne aka kira jami’an tsaro domin sanar da su faruwar al’amarin, lamarin da ya sa sojoji da jami’an wasu hukumomi suka garzaya wajen da abin ya faru.

Saidai, ƴan bindigar sun tafi da ita a lokacin da jami’an suka isa yankin.

Lamarin da ya sa jami’an sojoji da ƴan sanda suka ƙaddamar da atisayen farauto ƴan bindigar da ceto jami’ar.

By Babaji