Fushin miji na

Daga AISHA ASAS

Zamani ya kai mu lokacin da mata ke ganin damuwa da fushin miji zubar da aji ne. yayin da waɗansu ke kallon sa a matsayin rashin sanin ciwon kai. A cewar wasu ƙyale shi har ya gaji ya huce dan kan sa. Waɗansu matan kuwa cewa suke yi “idan ka nuna wa namiji ka na tsoron fushinsa to kin zama marainiyar shi. Kuma ai da ma namiji ba ɗan goyo ba ne. Kuma duk wadda ta ɗauke shi uba za ta mutu marainiya.”

To uwar gida, ya aka yi ki ka tsufa da gatanki a ƙarƙashin inuwar maigidanki? Ko shi ba namiji ba ne?

Annabin rahma ya ce “Da zan umurci wani ya yi wa wani sujada, da na umurci mace ta yi wa mijinta sujada”. Ba a ce ki yi ba, amma Annabin Allah na sanar da ke muhimmancin mijin ki cikin hikima, wanda ba tantama ya fi uba daraja. Domin da uba ne a sama da shi zai ambata.

Uwargida ki sani aure fa wani nau’i ne na ibada. Ita kuwa ibada ba a yi ma ta girman kai. Asali ma cikin ginshikan ibada ƙasƙantar da kai na ciki.

Ma su hikimar Magana dai sun ce, “Aure yakin mata”. ki ɗauki aure tamkar kina fagen yaƙi ne. Sara da suka duk za ki jure, ki tsaya a tsaye dan ganin ba ki faɗi ƙasa an take ki ba. Fatanki ki sami kutsawa komai wahala dan isa Aljanna.

Wallahi ‘yar’uwa babu faɗuwa dan kin ƙasƙantar da kanki dan rarashin mijin ki. Meye faɗar Manzon tsira ga mata? Ya ce, “Mace ‘yar Aljanna ita ce mai ba wa mijin ta haƙuri ko da ita ke da gaskiya”. Ma’ana a duk lokacin da mijin ki ya yi fushi to idan kina son samun Aljanna ta wannan ɓangaren ki ɗauki laifin ko da ba na ki ba ne. Ki ba shi haƙuri cikin ƙauli mai daɗi. Ba wai “to Ɗanlami yi haƙuri ba dan ka cancanci in ba ka shi ba. Don neman Aljanna, amma wallahi ban da haka………. hmmm! ai za mu haɗu a wani gurin.”

Wannan ba da haƙurin ko makamancin sa ba ya da amfani. Kuma kada ki yi tsamanin samun kanki a cikin masu samun wannan falalar.

Uwargida kina zaune, kin gama aikinki, kin yi wanka sai ƙamshi ke tashi kina jiran dawowar maigida. Duk wani abu da ya hane ki, ko ba ya so kin kawar da shi don gudun ɓacin ransa. Amma kwatsam ya faɗo falon tamkar wanda aka jeho shi. Fuska a ɗaure. Sai ya balbale ki da masifa. Laifin kuwa an ce masa an gan ki ƙofar gida kina kallon mazan mutane. Ko kin yi wa ƙawarki rakiya kun tsaya kan titi kuna dare-dare. Kuma ƙila ba ki ma san da wannan zancen ba, koma wani abu ya faru makamancinsa ba haka ya faru ba.

To a nan yana da kyau ki fahimci irin na ki mijin. Akwai namijin da idan ya na faɗa ya fison matar shi ta yi shiru ya yi ta zuba har sai ya yi mai isar sa. Hakan ne zai ba shi damar amayar da duk fushin nasa.

Akwai kuma wanda da ya fara ya ke so ki ta ba shi haƙuri har ya kai ƙarshe. Kuma akwai wanda idan ya hau ya fi so ki ƙyale shi har sai ya sauko.

To Hajiya Uwargida idan mijin ki na cikin na farko da muka lissafa, da ya fara ki sunkuyar da kai, ki yi ta sauraren sa. Kada ki ɗauki waya kina danne-danne, wannan alama ce ta kanka ake ji. Hakan zai iya ƙara hura wutar fushin nasa. Kuma kada ki tashi ki ba shi guri. Kuma kada ki yi abin da zai nuna hankalinki ba a kansa yake ba. Ki jure har ya kai ƙarshe. Da ya kammala ya ɗan sauko ke nan. Sai ki furta masa Kalmar ka yi haƙuri cikin sanyin rai da marerecewa. Ba ɗaukar lokaci mai tsayi zai sauko. Domin ire-iren waɗanan mazajen ba su cika riƙo ba.

Idan na ki na cikin layi na biyu kuwa, ko da ba ki yi laifin da ya ke tuhumar ki da shi ba ki yi gagawar zubewa a gabansa idan kuna keɓance. Idan a jama’a ne za ki iya ba shi haƙuri ko da da fuskar ki ne. ya danganta da muhalin da ku ke a lokacin faruwar al’amarin. Ka da ki yi ƙoƙarin sanar da shi gaskiyar zance dan zai iya ƙara hasala shi. Ki ba shi haƙuri cikin lafazi mai daɗi, tare da rarashinsa a yanayin da ya kamata. Idan abin na buƙatar ki fahimtar da shi, to bayanin zai biyo bayan nasarar shawo kansa ya daina fushin.

A lokacin ne zai saurare ki. Kuma a kwai yiwar ya fahimce ki. Idan ma bai aminta da zancenki ba ki bar ta a hakan. Ke dai kina da riba biyu don ba ki da hasara. Na farko, Allah Ya ga kyakyawar niyarki zai ku