
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya magantu kan tuntuɓe da ya yi yayin hawa motar zagaye a ranar bikin cikar demokradiyya shekaru 25 ganin yadda ɗaukar ta karaɗe shafukan sada zumunta da sauran gidajen jaridu.
A lokacin da yake magana wajen cin abincin bikin demokraɗiyya a daren Laraba a fadar shugaban ƙasa, Tinubu cikin raha yace, mutane sun gagara fahimtar rawar waƙar ‘Buga’ ce ko kuma gaisuwar al’ada ta ‘Idobale’ ce ya yi a lokacin aukuwar lamarin.
Shugaba Tinubu, ya ƙara da cewa, hakan na nuna farin cikinsa ga ranar demokradiyya da kuma girmama al’adar ƙabilarsa ta Yaroba.
