Ƙungiyar ƙwadago reshen Jihar Osun, ta ce za ta ɗau mataki a kan duk jihar da ta gaza biyan mafi ƙarancin albashin ₦70,000. Wannan ya fito ne daga bakin Mr Christopher Arapasopa a wata hira da yayi da manema labarai a birnin Osogbo.
Ya ƙara da cewa, a ƙungiyar ta ƙwadago ta amshi wannan ₦70,000 domin gujewa ƙarin farashin mai. Wanda yace, in haka ya faru to ƙarin albashi ba zai yi wani amfani ba, zai jefa yan Nijeriya cikin wata wahalar ba ma’aikata kaɗai ba.
Ya cigaban da faɗa, babu wani gwamna da zai ce ba zai iya biya ba. Domin tun muna tattaunawa da su, suke faɗin ₦70,000. Duk wani Gwamna da ya gaza biyan sabon mafi ƙarancin albashi, zamu ɗau mataki a kan shi a ƙungiyance kamar yadda muka faɗa.
