
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
An umarci bankunan Nijeriya da cibiyoyin harkokin kuɗi su mayar da ƙuɗaɗen asusun da aka daina amfani da su da waɗanda ba a bayyana mallakar su ba da wasu kadarori ga babban bankin Nijeriya, CBN.
Jawabin ya fito ne cikin wani saƙon umarni da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan sashen tsarin kuɗaɗe da gudanar da bankuna, John Onojah inda ya ce duk asusun da ƙuɗaɗen da ba a bayyana mallakar su ba da suka kai shakara goma, za a gadar da su ga asusu mai suna; ‘Unclaimed Balances Trust Fund Pool Account’ (UBTF).
Bankin ya ce, za a iya sanya kuɗaɗen a asusun adana kuɗaɗen kashewa na ƙasa da wasu harkokin tsaro na gwamnati kamar yadda dokar ire-iren kuɗaɗen gyaran watan Oktoba, 2015 ya nuna.
Haka kuma, yana daga cikin manufar aiki da dokar, mayar da ƙuɗaɗen ga masu su yayin da suka bayyana da kuma samar da wurin ajiyar ire-iren waɗannan ƙuɗaɗe.
Sannan, dokar ta bada damar naɗa kwamitin kula da asusun UBTF domin kula da tabbatar da kiyaye dokar gudanar da ƙuɗaɗen.
