
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin raba wutar lantarki na ƙasa, TCN, ya aika saƙon dakatarwa ga kamfanin lantarkin Abuja, AEDC kan zargin ƙin biyayya ga dokokin kasuwa.
TCN ya ce, AEDC ya gaza samar da tsarin gudanar da kasuwa da isasshen tabbacin shaidar banki kamar yadda sakin layi na 15.3.3 na dokar kasuwanci ya nuna.
Haka nan, an sanar da AEDC batun matsalar kuma an bashi kwanakin aiki biyar ya gyara ko kuma a sauke shi daga tashar.
Jawabin ya ƙara da cewa, wa’adin zai ƙare ne a ranar 28 ga watan Yuli, da tsakiyar dare.
Kazalika, AEDC ya sha samun sanarwar cike ƙa’idar wacce ya gagara yin gyara a kai, a sakamakon haka an dakatar da kamfanin daga tsarin kasuwancin lantarki. Sannan, a lokacin dakatarwar, babu wani ƙwantiragi ko yarjejeniya da za a shigar.
