Ganduje ya naɗa sabon Sarki a Gaya

Daga AMINA YUSUF ALI

A daren Asabar ɗin da ta gabata ne, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon Sarkin Gaya.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da naɗin a cikin wata sanarwar da safiyar ranar Lahadi.

Shi dai wannan sabon sarki, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ana ganin ya tsallake rijiya da baya ne, bayan ya ka da kusan fiye da mutane 40 waɗanda aka ce su ma suna zawarcin wannan kujera.

Kuma kafin naɗin sa, sabon Sarkin, wanda ɗa ne ga marigayi Sarki Ibrahim Abdulkadir, kirmau mai gabas da ya rasu ranar Larabar da ta wuce, shi ne ke rike da sarautar Ciroman Gaya.

Masarautar Gaya dai na ɗaya daga cikin sabbin masarautu huɗu da Gwamna Ganduje ya daga likafarsu a shekarar 2018. Inda suka zama masarautu masu daraja ta ɗaya.

A cewar sanarwar, “Gwamna Ganduje, ya yi amfani da damar da dokar masarautu ta Jihar Kano ta 2020 wacce aka yi wa kwaskwarima ta ba shi wajen na]in Alhaji Ibrahim Aliyu Abdulkadir a matsayin sabon Sarkin Gaya.