EFCC ta kama bokan da ya wanki majinyancin attajiri miliyan N16

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu haka dai wani ɗan damfara wanda ya wanke wani mutum mai neman ku]i har zunzurutun Naira miliyan 16 ya fa]a komar hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC.

Hukumar EFCC ɗin ta yankin garin Maiduguri ta samu nasarar damƙe wani wanda ya yi ikirarin shi boka ne, Mohammed Ibrahim, da kuma abokin aikinsa, a kan zargin wankiyar  Naira miliyan sha shida ga Mohammed Gaji.

Muhammad Ibrahim da Ibrahim Abubakar ana zargin su ne da amsar waɗancan maƙudan kuɗaɗe daga Muhammad a matsayin sadaka don a yi masa aikin da zai samu kuɗi. Inda hukumar EFCC ta cafke su a garin Sabon Bolori, Bayan Chad Basin, a jihar Borno.

A wani bayani da ya yi a ranar Talatar nan da ta gabata, mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwajaren ya bayyana cewa, abinda ya matsi bakin Muhammad Gaji har ya tona asirin damfarsa da aka yi shi ne, gurfanar da shi da aka yi a gaban kuliya a kan zargin sama da faɗi da kuɗaɗen wani Muhammad Bukar har Naira N22.2 da ya ba wa shi Gaji  domin ya haɗa masa garken kiwon shanu.

Jami’an tsaro suka cafke shi, kuma suka cigaba da gudanar da bincike har ma suka matse shi, sai Muhammad Gaji ya tona wa kansa asiri cewa, maimakon ya haɗa wa Bukar garken kiwon shanun kamar yadda suka yi, sai ya yi rub da ciki a kan waɗancan N22.2 ɗin. Inda har ma ya bai wa Muhammad Ibrahim da Ibrahim Abubakar Miliyan 16 domin su yi masa aikin da zai zama mai kuɗi.

Gaji ya ce, bokayen ƙaryar sun ba shi wani dutse mai daraja, sannan an ba shi kuma wani ƙaramin akwatin ƙarfe mai ɗauke da farin yadi da kuɗin ƙasar waje a cikinsa. Sannan kuma sun umarce shi da ya yi azumi na tsahon watanni uku da kwana ɗaya, sannan buƙatarsa za ta biya.

Uwajaren ya bayyana cewa, a lokacin da jami’an nasu suka kai farmaki a gidan masu ikirarin bokancin, sun ci karo da wani ƙaton rami a ƙarƙashin teburi wanda aka lulluɓe da fatar dabbobi wanda a nan abokin aikin Muhammad yake ɓuya yana wa mutane magana a matsayin aljani.

Sannan kuma an samu fararen yadudduka da  rubuce-rubucen larabci, ƙwore, fatun dabbobi, ƙahonnin dabbobi da kuma kuɗaɗen ƙasar waje sai akwatunan ƙarfe  guda biyu ƙanana.