Tsohon Sarkin Kano ya ziyarci Sarkin Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Sheikh Inyass, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi ll ya kai ziyara a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III.

Yayin ziyarar, Khalifa Sanusi ya bayyana Sarkin Musulmin cewa, shi da tawagarsa sun zo fada ne domin yin gaisuwar ban girma da kuma neman sanya albarka, da ma gabatar wa Mai Alfarma takardar da aka bai wa Mai Martaba Sarki Sanusi na Khalifancin Ɗarikar Tijjaniyyah ta Nijeriya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Sheikh Inyass, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi ll a fadarsa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi lale marhabin da dawowar Mai Martaba a gida, domin kuwa Sakkwato gida ce a gare shi.

“Tabbas ka cancanci wannan matsayi da Allah ya baka kuma za ka iya ɗaukar wannan nauyin da aka ɗora maka.

“Ina roƙon Allah subhanahu wata’ala da ya ƙara haɗa kan al’ummar musulmi duk inda su ke, domin su zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya”, inji shi.