‘Yan bindiga ba su da addini, kamar dabbobin daji su ke – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya bayyana cewar, ‘yan bindigar da ke aikace-aikacen ta’addanci a jihohin arewa maso yamma kamar dabbobin daji su ke, kuma mutane ne waɗanda ba su da addini ko alƙibla.

“Aikace-aikacen ‘yan bindiga a jihohin arewa maso yamma da wa su sassan Arewa ta tsakiya ya sauya zuwa aikin ta’addanci, saboda haka mun fito da dabaru daban-daban don yaƙar wannan musiba.

“Waɗannan mutane ba su da aƙida ko addini ko kuma alƙibla, kamar dabbobin daji suke”, inji Masari.

Gwamna Masari yana magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Muhammed a wata ziyarar aiki da ya kawo jihar Katsina.

Masari ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai dabar ‘yan bindiga fiye da 150 a dazuzzuka ƙarƙashin shugabancin ‘yan bindiga daban-daban.

Ya ƙara da cewa, jihohin Arewa-maso-yamma guda bakwai da kuma Arewa ta tsakiya sun amince da ɗaukar ‘yan sa kai guda dubu uku a jihohin su don taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro musamman ‘yan bindiga da ma su garkuwa da mutane.

Gwamanan ya kuma tabbatar da cewa gwamnonin jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Neja, Katsina da Nasarawa sun yi taro inda suka amince da ɗaukar ƙungiyoyin ‘yan sa-kai aiki domin taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi jihohin.

A cewar Masari, jami’an ‘yan sandan ƙasar nan ne za su horar da ‘yan sakai da za a ɗauka kuma su ne za su taimaka wa hukumomin tsaro.

Masari ya ƙara da cewa, “Ina magana ne a madadin jihohin da aka ambata.

“Haƙiƙa ya kamata su kasance a wannan taron tuntuɓa da mu ke gudanarwa a nan Katsina, amma ina magana a madadin su.”

Haka zalika, gwamna Masari, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta saka jihar Katsina cikin jihohin da take ba tallafi domin tunkarar ƙalubalen rashin tsaro tare da rage nauyin da gwamnatin ke ɗauka dangane da tsaron jihar.

A cewar gwamnan,  jihar tana kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tallafa ma hukumomin tsaro da suke aiki a sassa daban-daban na jihar, wanda ba don wannan tallafin da gwamnatin ke bayarwa ba, tabbas da ayyukan su sun tsaya.

Daga ƙarshe Masari ya bayyana cewar yaƙi da ta’addanci da ake yi a halin yanzu alhakin kowa da kowa ne, saboda haka ne ya yi kira ga ‘yan ƙasar nan da su kasance ma su bayar da gudummawar su ga hukumomin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *