Tattalin arzikin Nijeriya na dab da rushewa – Sanusi II

Daga SANI AHMAD GIWA

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya ce, tattalin arzikin Nijeriya yana dab da rushewa.

Sanusi ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi na ranar rufe gagarumin taron hannayen jari da aka yi a Kaduna mai taken KADINVEST 6.0, Sanusi ya ce baya ga cewa Nijeriya tana da matsala wurin samar da mai, a yanzu kasuwannin duniya ba su siya.

Ya ce makomar ƙasar nan ta dogara ne da tattalin arziki mai dogaro da ilimi, kuma Nijeriya an bar ta a baya a cikin ƙasashen Afrika masu dogaro da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

Sarkin ya jajanta yadda ya kasance ƙasar Ghana mai ƙaramin tattalin arziki ke zuba hannayen jari a fannin ilimi amma Nijeriya ke zuba kashi 7 na kasafinta a ilimi.

“Mutum takwas kacal a cikin ɗari na ‘yan Nijeriya da suka fara karatun firamare ke kammalawa har zuwa jami’a.”

“A faɗin duniya, aiki ya sauya fasali; kashi talatin zuwa arba’in na ma’aikatan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki suna ƙoƙarin inganta fasahar su zuwa 2030. Amma kuma ta yaya ake samun wannan sauyin? Ilimin fasahar sadarwa da kuma aiki daga gida wanda muka gani yayin annobar Korona.

“Nan ba da daɗewa sakako za su koma yin ayyuka a ƙasashe masu yawa kuma waɗanda za su yi aikin za su kasance masu sarrafa sakakon, samar da su ko kuma gyara su.

“A watanni kaɗan da suka gabata, ƙasar Jamus ta samar da makamashin da ake sabuntawa domin buƙatar dukkan ƙasar. A yau muna samun matsala wurin sayar da man fetur a Nijeriya. Ba matsalar samarwa kaɗai ba, har kasuwa babu.

“Don haka, wannan sauyi ne na dole kuma a matsayin na ƙasar da ta dogara da man fetur, ya dace abubuwa su sauya.”

“Nijeriya ita ce ƙasa ta 114 a duniya cikin kasashen da ke harkar kasuwanci da sana’o’i. Mu ne na ƙasa sosai a ƙasashen Afrika kamar Kenya, Rwanda da kuma Senegal. A takaice dai muna ƙasa ta 14 a kasashen Afrika. Ina ganin ya kamata mu gane wannan, kuma mu duba yadda ƙasar tamu take, mu ma daina yekuwar kiran ƙasar tamu a matsayin giwar Afrika.

“Ƙasashe kamar irin su Kenya, Ruwanda da Senegal duk suna gaban mu nesa ba kusa ba. Ba ina maganar ma ƙasar Afrika ta Kudu ba ne. Abinda za mu kasashe akan ilimi kashi 7 ne kawai cikin ɗari na kasafin kuɗin mu a shekara guda kawai, amma ƙasar Ghana wadda ba ta da tattalin arziki kamar Nijeriya, kuma kuɗin shigar da ƙasar ke samu ko kusa bai kai yadda Nijeriya ke samu ba, amma Ghana tana kashe kuɗi a fannin ilimi fiye da Nijeriya.

“Sannan abin mamaki ana ta ɗauke kamfanoni da masana’antu zuwa Ghana. Mun yi mamakin yadda Shugaban Kasar Ghana ya zama shi ne jagoran shugaban Afrika. Sam ba ma ƙoƙari wajen zuba kuɗaɗe a harkar ilimi da kuma gina al’umma.”

Tsohon Sarkin Kano na 14, ya kiara jaddada cewa akwai buƙatar ƙirƙirar fasaha domin matasa wanda zai samar da muhallin havakar tattalin arziki da ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *