Ko a masallacin Makka da Madina ba zan nemi gafarar Masari ba, cewar Mahdi Shehu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kamfanin Dialogue Group, Shehu Mahdi, ya ƙaryata wasiƙar neman afuwar Gwamnan Katsina, Bello Masari, kan batun yaɗa bayanan bogi a kansa da aka ce ya aika wa gwamnan.

A ranar Alhamis, 23 ga Satumban 2021 aka ga bayyanar wata wasiƙa ta neman yafiya zuwa ga Gwamna Masari da ma al’ummar jihar wadda aka ce Mahdi ne ya rubuta tare da aikawa da ita ga gwamnan.

Sai dai, cikin wani saƙon bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa mai tsawon minti 10, an ga Shehu Mahdi na bayani cikin harshen Ingilishi inda ya ƙaryata wasiƙar, yana mai cewa ko kaɗan ba shi ya rubuta wasiƙar ba. Ya ce wannan ba komai ba ne face aikin wasu da ba su manufa balle buri a rayuwa.

A cewar Mahdi, da farko bai so cewa komai a kan wasiƙar ba, amma domin wayar da kan ɗimbin masoyansa shi ya sa ya fito ya ƙaryata wasiƙar.

Ya ce hatta takardar da aka rubuta wasiƙar a kai ba ta kamfaninsa ba ce kamar yadda aka yi iƙirari, balle kuma samfurin sa hannun da ke cikin wasiƙar, wannan ma ya ce ba sa hannunsa ba ne

A cewar Mahdi, shi bai ga yadda za a yi ya rubuta irin wannan wasiƙar ba sanin cewar sun shiga kotu kan batutuwan da wasiƙar ta ƙunsa.

Haka nan ya ce, shi mutum ne wanda muddin ya san cewa yana kan hanyar da ta ce kan wani al’amari, to, ko ta halin ƙaƙa zai ci gaba da gwagwarmaya ba tsoro ba ja da baya har sai ya cimma ƙudirinsa. Ya ce shi ba wawa ba ne da zai fito ya bai wa Masari ko wani jami’in gwamnati haƙuri, yana mai cewa matsayinsa ya zarce haka.

Ya ci gaba cewa, ya gamsu kan cewa duk waɗanda suka yi masa farin sani, ya tabbata ba za su taɓa yarda da wancan wasiƙar bogin da aka fitar da sunansa ba.

Mahdi ya ƙara da cewa, shi fa a halin da ake ciki, “Da a ce zan haɗu da Bello Masari, ko El-Mansuk, ko Mustapha Inuwa Masallacin Makka, ko Madina, ko kuma Baitul Muƙaddas don aikin Hajji ko makamancin haka, sanan dukkansu ko ɗayansu ya yi mini sallama, ba zan amsa sallamar ba.

“Haka ma ko hannu suka miƙo mini don yin musabaha, ba zan karɓa ba saboda ban yarda da su ba.”

Ya ci gaba da cewa, “‘Yar tsamar da ke tsakanina da su ta har abada ce. Kuma shekaruna sun wuce na bada haƙuri a inda bada haƙurin bai da wani amfani. Babu wanda ya isa ya yi mini wata barazana a wannan shekarun nawa.”

Mahdi ya kammala saƙon nasa da roƙon Allah kan duk wanda ke da hannu cikin wannan wasiƙar bogin, Allah ya jarabce shi da masifa kan masifa, baƙin ciki kan baƙin ciki, cuta kan cuta, hasara kan hasara da sauransu.