Ganduje ya shigar da sabuwar ƙara a kan Jaafar

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sake maka mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, a kotu kan wani sabon ƙorafi.

Ganduje ya sake shigar da ƙara kan Jaafar Jaafar ne tare da kamfanin Penlight Light Media Limited a wata Babbar Kotun Abuja inda da aika wa waɗanda lamarin ya shafa da takardar sammaci mai ɗauke da lamba CU/1598/2021 da kuma kwanan wata 15, Yuli, 2021.

Wa’adin amfanin sammacen wata uku ne daga ranar da aka ba da shi, kamar dai yadda rajistaran Babban Kotun Abuja ya sanya hannu.

Idan dai za a iya tunawa, a can baya Ganduje ya maka Jaafar Jaafar a wata Babbar Kotun Kano inda ya buƙaci a biya shi diyyar biliyan N2 saboda ɓatanci da ya ce Jaafar ɗin ya yi masa a jaridarsa da yake yaɗawa ta intanet inda ya wallafa wani hoton bidiyo da ya nuna Ganduje na cika aljihunsa da dala na kwangilar da aka bayar a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *