Garin Bauchi zai samu tagomashin sabon gidan radiyo da talabijin

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Wani kamfani mai zaman kansa da ake wa laƙabi da ‘Eagle Broadcasting Corporation’ zai kafa gidan radiyo a garin Bauchi. Haka ya biyo bayan sahalewar da Shugaban Ƙasa, Muhammdu Buhari ya yi da lasisin kafa gidan radiyon.

Wannan kyakkyawar niyya tana ƙunshe cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai da mashawarcin kamfanin, Abdul Ahmad Burra ya fitar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewar, Shugaban ƙasa ya sake amincewa da kafa wani sabon gidan Talabijin mai dogon zango zuwa ƙasashen ƙetare, (International Television Station).

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince wa kamfanin ne ya kafa gidan radiyo mai zaman kansa da aka yi wa suna ‘Eagle Radio’ a garin Bauchi.

“Lasisin da Shugaban Ƙasa ya amince wa shi ne na kafa tashoshin radiyo da talabijin a sassan ƙasar nan. Hukumar Kula Da Lamuran Kafofin Watsa Labarai masu sauti (NBC) shi ma ya amince wa kamfanin da kafa babbar tashar talabijin mai dogon zangon shiga ƙasashen ƙetare da ake wa laƙabin ‘Eagle TV’ a nan garin Bauchi.

“Aniyarmu ta tsumduma cikin wannan aiki na watsa labarai ya biyo bayan kwaɗayi da kamfanin namu ya yi na cike giɓin sadarwa da yake a wawake a sassan ƙasar nan”, Inji Burra.

“Har wa yau aniya ce da za ta bai wa waɗannan kafofi na watsa labarai kasancewa majiya ga al’umma, ta samar wa ‘yan ƙasa wata madogarar yin sulhu kan lamura a tsakaninta yadda za su cimma burikansu na rayuwa, haɗi da samar wa ‘yan ƙasa hanyoyin ayyukan ƙwadago”.

Gidan radiyon ‘Eagle Radio’ da za a kafa a garin Bauchi zai yi amfani da kayayyakin fasahar zamani na sadarwa wajen gabatar da saƙonninsa, da suka haɗa da labarai, shirye-shirye, da nishaɗantarwa, da sauransu, ga jama’ar Jihar Bauchi da kewayen ta”, kamar yadda sanarwar ta ce.

Kamfanin ya bayyana cewar, kafar ‘Eagle TV’ kafa ce ta yaɗa shirye-shiryensa da suka haɗa da labarai, zaurukan tattaunawa da ma ƙasidoji ta cikin harshen turanci a kan dukkan lamuran da suka shafi ƙasa da ma duniya bakiɗaya.

Burra ya bayyana cewar, hukumar lura da kafofin watsa labarai ta hanyar sauti (NBC) ce ta bai wa kamfanin lasisin  fara ayyuka na wucin gadi. Kuma yanzu haka, ana kakkafa turakuna da na’urorin ya]a labarai masu ingantattun sautuka.

Yayin da yake ƙarfafa aniyar wannan kamfani na kafa tashoshin watsa labarai dake kan hanyar kammaluwa, Burra ya bayar da tabbacin cewar, tashoshin za su samu tagomashin ƙwararru bisa ayyukan yaɗa labarai, da za su huce wa jama’a haushin nakasun sadarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *