Ya kamata gwamnatoci su kafa masana’antun koya sana’o’i a gidajen yari – Doguwa

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Muƙaddashin Kwanturola na gidan gyara jalin da ke Bauchi, Musa Dauda Doguwa ya buƙaci gwamnatocin lardin arewacin ƙasar nan da su kafa ma’aikatu na koya wa matasa sana’o’i da zummar rage gararambar su.

Doguwa ya bayyana cewar, ya yi ayyuka a gidajen gyara hali daban-daban da ke sassan ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da na Kano, Jigawa, Neja, Kaduna, Katsina, da sauransu. Amma bai taɓa iske gidan maza da yake da tarin matasa kamar na Bauchi ba.

Doguwa ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan da kwamitin da ke bibiyar lamuran mazauna gidajen gyara halin ya kammala ziyarar aiki na kwanaki biyu a jihar. Wato wacce ya yi a kwanakin baya.  Doguwa ya ƙara da cewa, ya yi ta’ajibin yadda ma fi yawan mazauna gidan na gyara halin da ke Bauchi dukka matasa ne.

“Abinda ya fi ba ni takaici da zuwa na garin Bauchi, gaskiyar magana shi ne, akwai buƙatar ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi ta janyo hankalin gwamnatin jiha. Duk jihohin da na lissafa, ban taɓa zuwa jihar da za ka shiga gidan kurkuku ka tarar da matasa zalla ‘yan shekara 18 zuwa 25 su ne ma fi yawa a gidan ba”. Inji shi.
 
Doguwa, wanda shi ma ɗan kwamitin bibiyar lamuran mazauna gidan mazan ne, wanda babbar mai shari’a ta jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ke jagoranci, ya ce: ma fi akasarin mazauna gidan na gyara halin dake Bauchi sun aikata manyan laifuka ne kamar fashi da makami, fyaɗe, satar mutane domin neman kuɗaɗen fansa, da sauransu.

“Idan muka duba, za mu ga cewar, gaskiyar magana ita ce, Jihar Bauchi akwai matsala wacce take buƙatar a duba, duba irin na natsuwa, a samar wa matasa abubuwan yi, a madadin gararamba da suke yi suna aikata manyan laifuka”.

Doguwa ya ƙara da cewar, abin takaici ne cewar, waɗannan matasa ba su da niyyar yin karatu, kowa so yake yi ya samu kuɗi cikin sauƙi, kuma da gaggawa. Ga shaye-shaye da barikanci a cikin gari, musamman garin Bauchi.

A cewar sa, “Akwai buƙatar gwamnati ta samar da ainihin ma’aikata, ta koyar da sana’o’i, a kuma kafa cibiyarta a kowace mazaɓa da ke cikin jihar bakiɗaya. A riƙa koyar da su ana yaye su da madafar sanin sana’a, yadda za su yi dogaro da kansu, har ma su koyar da wasu.

Ya ce, “Akwai buƙatar a kafa cibiyar koyar da sana’o’i a kowace mazaɓa ta jihar Bauchi, a kange matasan tamkar makarantun kwana na ɗalibai. Ana ciyar da su abinci tare da ba su horaswa. Yadda kowanne zai yi tutiya da sana’ar da ya koya domin dogaro da kai.  Kuma hakan ita ce mafita.

“Idan muka koma batun arewacin ƙasa bakiɗaya, muna cikin tashin hankali. Shelar a ware da Inyamurai da Yarabawa suke yi, wallahi suna ɓata lokacinsu ne. Domin sun riga sun ci mu da yaƙi.

“Maganar wai suna so su ware, ba sai sun ware ba, ka je duk wata Babbar makaranta da take Arewa ka duba ainihin yawan ɗaliban makarantar, za a ga kashi 75 cikin ɗari ‘yan kudu ne, kashi 25 cikin ɗari kaɗai ne ‘yan Arewa.

“Idan ka je kudancin ƙasar nan, ka duba makarantunsu. Ka je Nsuka ko Legas, ka ce a kira maka ‘yan Bauchi, ba za ka samu mutum biyu ba. Ba wanda yake zuwa can karatu. Amma su sun cika makarantunsu, sun zo sun cika namu, me wannan yake nunawa?”

Doguwa ya ƙara da cewar, “Wallahi ya kamata mu tsaya, mu yi wa kanmu faɗa. Shugabanninmu su duba, a yi nazari a kan wannan al’amari.”

Doguwa ya bayyana cewar, gidajen gyara halin na kudancin ƙasar nan, idan mutum ya je, zai iske tsofaffi ne a ciki. Domin duk matasansu suna karatu a makarantu, amma namu matasan sun tasar ma lalacewa, kuma babu wanda yake duba wannan lamari.

Doguwa sai ya bayyana cewar, “Da wannan nake jan hankulanmu a kan cewa don Allah, don Annabi, haƙƙi ne a kanmu, mu shugabanni, a tsaya a yi nazari a kan abubuwan da na zayyana”.

Muƙaddashin Kwanturolan ya kammala jawabin sa da cewar, “Allah ya dafa mana, Allah ya taimaki ma’aikatar shari’a ta Bauchi, ya taimaki jihar Bauchi da ƙasa bakiɗaya, Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah ya gyara zukatanmu bakiɗaya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *