Gaza: Burin Isra’ila ya cika?

Spread the love

Hare-haren da Isra’ila ke faɗaɗawa daga yaƙin Gaza na nuna muradun Isra’ila na murƙushe duk mai adawa da ita. Dama gwamnatin Isra’ila ta Firaminista Benjamin Netanyahu ta hada gamaiya ta ‘yan ina da yaƙi. Wasu masu tsaurin ra’ayin Yahudanci ne ke cikin gwamnatin kuma har barazanar za su fice daga gwamnatin su ke yi ga duk wani yanayi na nuna ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Hatta shi kan sa Netanyahu da ya fi kowane Firaminista yawan zama kan kujerar mulki na kare muradun sa na siyasa ta hanyar tabbatarwa Isra’ilawa cewa zai gama da Hamas har ma da duk masu marawa Hamas baya. Netanyahu zai kara matsa ƙaimi ne wajen yaƙin don a ƙara sallama ma sa da ba shi kambun baraden Yahudu masu iya ɗaukar matakin gayawa jini na wuce kan duk masu dagawa ƙasar yatsa. Ba ma nan gwamnatin Isra’ila ta Tel’aɓiɓ ba, jagoran Yahudawan na son sayawa jagororin duniya masu mara ma sa baya yabo a ƙasashen su cewa su na dafawa jan gwarzan kare Isra’ila. Matakan ma na Netanyahu na samun cikas don rashin nasarar yunƙurin da ya yi na jefa sashen shari’ar ƙasar a aljihun gwamnati ta hanyar neman mayar da gwamnati gagarau ta aikata abun da ta dama amma shari’a ko alƙalai ba su da uffan a kai. In an tuna yunƙurin ya haddasa zanga-zanga daga ‘yan ƙasa da ke ganin hakan neman wuce gona da iri ne ko ƙoƙarin maida alƙalai ‘yan amshin shatan sashen zartarwa. Firaministan na fuskantar zargin cin hanci da rashawa da ya ke ta fafutukar korewa amma da alamun zargin zai sake dawowa nan gaba. A yanzu dai Netanyahu na yi wa Isra’ila sashen abun da su ke so duk da ba duka ba. Muradin Yahudawa shi ne karɓo sauran waɗanda Hamas ke riƙe da su daga harin ranar 7 ga Oktobar bara.

Yanzu an shiga makon cika shekara ɗaya cif da fara shata dagar yaƙin nan Gaza. Ba lallai Hamas ta gagari Isra’ila ba ne amma akwai dalilan da ke kawo tsaiko wajen murƙushe ƙungiyar bisa muradaun Isra’ila. Fitattu daga dalilan sun haɗa da bi cikin dabaru don karɓo ko kwato sauran kamammun da ran su. Kwanaki an samu wasu daga ciki a mace da hakan ya kawo tsananin bakin ciki a Isra’ila. Abu na biyu Isra’ila ba ta son ta kashe kowa a Gaza don kar ta kunyata manyan ƙasashen da ke mara ma ta baya da ke tutiyar ‘yanci inda akisan kare dangi zai hana su kwarin guiwar nunawa duniya su ɗin masu kare ’yancin dan adam ne. Abu na uku matuƙar fin karfin ko cin zalin ya kai wata ganiya dole wasu kasashe za su saka baki ko juyawa Isra’ila baya ko da a fatar baki ne. Isra’ila na son kafa hulɗar jakadanci da sauran ƙasashen Larabawa musamman Saudiyya don zama daram a yankin amma aƙalla Saudiyya ba za ta amince ba in an shafe Gazawa daga doron ƙasa. Duk yawan kasashen da za su ƙulla jakadanci da Isra’ila tsakanin Larabawa ba za su wadatar da Isra’ila ba sai ta samu kan Saudiyya.

A na ta ɓangaren Saudiyya na takatsantsan wajen riƙe kambun ta na jagora a tsakanin Larabawa don haka ta ke jan kafa wajen hulɗa daIsra’ila kai tsaye. Ataikace kowace kasa na da siyasa da muradun ta a duniya fiye da yanda masu wata aƙida ɗaiɗaiku ko tausayi ke son lamura su faru bisa hasashe ko hangen da ba a gwamnatance ba. Ba na ganin a wannan zamanin Larabawa za su iya hada kai don yaki da wata kasa da ke mu su barazana. Yadda daidaiku masu hukunci da shauki ke son Larabawan su aukawa Isra’ila ba haka tsarin gwamnati ya ke ba a muradun siyasar duniya. Gaskiya siyasar duniya na da na ta amfani wajen kare shugabanni ko gwamnatocin ƙasashe da dorewar dangantaka da kawayen sun a tsaro da tattalin arziki. Tsarin gwamnati ya yi bambanci da matakan ƙungiyar mayaka kamar Hezbollah, Hamas, Houthi da sauran su.

Gwamnati ba za ta iya yaƙin sari-ka-noƙe ba kamar ƙungiyoyin mayaka sai dai a buga har a yi nasara ko a gama da gwamnatin ko shugaban ƙasar. Mu duba misalan yanda Amurka ta jagoranci ƙasashen taron dangi su ka ƙaddamar da yaƙi kan Iraƙi da a ƙarshe a ka kifar da gwamnatin Bagadaza har ma da yankewa da zartar da hukuncin kisa kan shugaba Saddam Hussaini.Mu duba yadda a ka kutsa Libya har a ka kashe marigayi Moammar Gaddafi. Mu tuba yanda Ayatullahi Khumaini ya jagoranci juyin juya hali kan gwamnatin shugaba Reza Fahlaɓi a 1979. Koyon darasi kan sa gwamnatocin ƙasashe ba sa marmarin shiga yaƙi kai tsaye sai ta amfani da wasu ƙungiyoyi kamar yadda Iran ke yi. Ko hare-hare da Iran ta kai kan Isra’ila ba ya na nuna ƙaddamar da yaƙi ba ne sai dai ramuwar gaiya na lokaci ɗaya.

ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon mai samun goyon bayan Iran ta tabbatar da kashe jagaoranta Hassan Nasrallah.

Marigayin ya rasa ran sa ne a harin da Isra’ila ta kai kan hedikwatar ƙungiyar da ke kudancin babban birnin Lebanon, Beirut.

Harin ya zo ne daidai lokacin da jagororin Hezbollah ke gudanar da taro a helkwatar inda maƙamin da Isra’ila ta yi amfani da shi ya ruguza ginin mai hawa 6.

Kazalika kwamandan Hezbollah na kudancin Lebanon Ali Karki ma na daga cikin waɗanda su ka mutu inda mutum 90 su ka samu raunuka.

Duk da wannan gagarumin koma baya, Hezbollah ta kara lasar takobin cigaba da yaƙi da Isra’ila da kuma marawa Falasɗinawa baya.

Nasrallah wanda ya jagoranci Hezbollah fiye da shekaru 30 na kan gaba cikin waɗanda Isra’ila ke son kashewa.

Hezbollah ta lashi takobin gwabzawa da maganin Isra’ila matuƙar ta shigo yaƙi ta doron ƙasa ba kamar yadda ta ke amfani da jiragen yaƙi ba.

In za a tuna a makon jiya Isra’ila ta kai mummunan hari ta jirgin yaƙin F 15 kan helkwatar Hezbollah da ke Dahiyeh a kudancin babban birnin Lebanon, Beirut inda shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah ya rasa ran sa.

Mataimakin shugaban Hezbollah Na’im ƙassim ya baiyana shirin na dakarun Hezbollah a jawabin farko da ya gabatar bayan rasa Nasarallah.

ƙassim ya gabatar da jawabin ne daga wani waje da ba a bayyana ba ya na mai ƙarfafa cewa za su gwabza da sojojin na Isra’ila.

Kalaman na zuwa daidai lokacin da Isra’ila ke cigaba da kai hare-hare a sassan Lebanon cikin mako biyu da hakan ya yi sanadiyyar rasa ran kwamandoji da dama na Hezbollah.

Gwamnatin Lebanon ta ƙara da cewa baya ga kwamandojin, kimanin farar hula 1000 na Lebanon ma sun rasa ran su daga hare-haren inda miliyan ɗaya su ka arce daga gidajen su.

Bayanaai daga Isra’ila na tabbatar da ƙasar Iran ta harba makamai fiye da 100 masu linzami cikin ƙasar ta Yahudawa.

Hakan ya zama martani ko ramuwa ga abun da Iran ta zayyana da kisan gilla da Isra’ila ta yi wa shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a Tehran da ma kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah a Beirut.

Iran ta gargaɗi Isra’ila da kar ta maida martani kan wannan harin don ramuwa ce kan hare-haren Isra’ila.

Haƙiƙa ko dai an kakkabo wasu daga maƙaman masu linzami da alamu akwai waɗanda su ka sauko a cikin Isra’ila.

Haƙiƙa harin ya zama bazata daga Iran da a ke ganin ta na ɗaukar duk wani matakin takatsantsan na fito na fito da Isra’ila don gudun kar hakan ya jawo ma ta aukawa yaƙi da ƙasashen yamma.

Bayan kisan Nasrallah Iran ta ce ba za ta yi yaƙi da Isra’ila ba amma ta na da tabbacin Hezbollah na da ƙarfin tunkarar Isra’ila.

Za a yi ta bitar abubuwan da ke faruwa da gano irin tasirin da harin na Iran ya yi don kuma ba lallai ne a samu wasu bayanai masu yawa ba daga Isra’ila da su ka wuce harin bai yi wani tasiri ba.

Yanzu dai an tabbatar daga tarihin tsarin Isra’ila za ta iya maida mummunan martani.

Dalilin harin ya sa Iraki rufe sararin samaniyara ta na wani lokaci amma daga bisani an bude don zirga-zirgar jirage.

Rahotanni na baiyana garzayawa da shugaban addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei zuwa wata maboya mai tsananin tsaro.

Wannan haƙiƙa ya biyo bayan barazanar Isra’ila ce da ta biyo bayan harin da ya kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah ta yanayi mai ban tsoro.

Yanayin hare-haren Isra’ila ta amfani da na’urorin sirri ya sa ba mamaki ko kaɗan in Iran ta dau tsauraran matakan tsaro kan jagoran na ta.

Wasu magoya bayan Iran da masu sharhi na tababar ba mamaki hatta hatsarin jirgin da ya kashe shugaban Iran Ebrahim Raisi na da alamar ayar tambaya.

Ayatollah Khamenei ya buƙaci musulmi su kaddamar da matakai kan Isra’ila da ke kai hare-hare da yin kememe wajen ƙin dakatar da yaƙin Gaza.

Kammalawa;

Sojojin Isra’ila sun kutsa yankin kudancin Lebanon da zummar gudanar da yaƙi ta ƙasa da mayaƙan Hezbollah.

Hukumar tsaron Lebanon ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila da ta zayyana da abokan gaba sun keta kan iyaka su ka shiga har tsawon mita 400 cikin Lebanon din.

Isra’ila ta shiga garuruwan kan iyakar da dama ta gargaɗi mazauna yankin su kaura don hare-hare da za ta kawo.

Da farko sojojin na Isra’ila sun fice daga yankin su ka koma cikin ƙasar su amma zuwa Laraba su ka juyo da tunanin komai lafiya ashe ‘yan Hezbollah sun yi kwantan bauna su ka buɗe wuta kan sojojin har sojan Isra’ila 4 ko 8 su ka mutu sannan sojoji 20 su ka samu raunuka.

Isra’ila na bayyana cewa ta na ɗaukar waɗanda su ka samu raunuka don garzayawa da su asibiti a yanayi mawuyaci da harbe-harben bindiga.

By ukarofi