Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gidauniyar ADG Care Foundation ƙarƙashin jagorancin Injiniya Rabiu Aliyu, ta tura wakilcin Daraktan Kula da harkokin sadarwa da Hulɗa da Jama’a Aliyu Abdul Garo, da Amina Tegal, domin cika alƙawuran da ta ɗauka na biyawa wasu daga cikin ɗaliban makarantar Goɓernment Girls Secondary School dake Garo kuɗin zana jarrabawar kammala karatun Secondary wato NECO.
Gidauniyar ta yi wa wasu daga cikin ɗaliban alƙawarin biya musu kuɗin zana jarrabawar sai dai kuma bayan fitowar jarrabawar ƙualifying sai ɗaliban suka samu nasarar cin jarabawar.
Hakan ya sa gwamnatin jiha ta biyawa wasu daga cikin su kuɗin, ita kuma gidauniyar ADG Care Foundation ta biya musu ragowar kuɗaɗen da yakamata su ƙarasa biya.
Hakazalika gidauniyar ta karɓi sunayen dukkanin ɗaliban da suke son cigaba da karatu kuma suka zana jarrabawar share fagen shiga jami’a wato JAMB domin tallafa musu wajen samar musu da gurbin karatu kyauta a dukkanin makarantun da suka nema.
Daga ƙarshe gidauniyar ta kai ziyara makarantar mata da take kusa da makarantar firamare ta Abdun Garo, domin ganin halin da suke ciki tare da tallafawa wasu daga ciki kayayyakin koyo da koyarwa, domin inganta karatunsu.
Gidauniyar ADG Care Foundation ta yi kira tare da jan hankalin waɗannan ɗalibai da su ci gaba da mai da hankali, domin samun ingantaccen ilimi tun daga tushe.
Sannan su ma ɗalibai da malaman makarantun sun jaddada godiyarsu ga gidauniyar ADG Care Foundation bisa irin ƙoƙarin da gidauniyar ke yi wajen samar da ayyukan cigaba ta kowanne ɓangare a wannan yanki.
