Gidauniyar Bintu Aliyu ta wayar da kan matasa masu shaye-shaye a Jos

Spread the love

Daga HABU DAN SARKI a Jos

Wata ƙungiya mai tallafawa mabuƙata da wayar da kan matasa, mai suna Bintu Aliyu Foundation ta shirya wani taron faɗakar da matasa maza da mata da ke tu’ammali da miyagun ƙwayoyi, domin fahimtar da su illolin shaye-shaye da muhimmancin sanin ciwon kansu.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagaroncin wakilan Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa ta NDLEA da ke Jihar Filato, waɗanda suka gudanar da faɗakarwa game da illolin da shaye-shaye ke yi wa lafiyar matasa da rayuwarsu. Yayin da suka baje-kolin wasu sinadaran kayan sa maye da suke kamawa a hannun matasa, don nuna wa matasan abubuwan da suke yi da ke cutar da rayuwarsu.

Shugabar ƙungiyar, Malama Zulaikha Abdullahi ta bayyana cewa, manufar ƙungiyar na ganin rayuwar matasa ta zama mai amfani da inganci ya sa ta shiga lungunan da matasa masu shaye-shaye suke tana fito da su da basu taimakon da suke buƙata, don su gyara makomar su. Ta kuma yi alƙawarin ɗaukar nauyin koya wa wasu daga cikin su sana’o’in dogaro da kai, don su daina zaman banza.

Wani ɗan jarida mai wayar da kan jama’a da taimakawa matasa kan inganta rayuwa, Abba Abubakar Yakubu, shi ma ya ƙalubalanci matasan da su yi wa kansu faɗa su kuma ƙauracewa mugayen abokai, da neman sana’ar da su riwe kansu da ’yan uwansu, da neman shawarar ƙwararru kan yadda za su raba kansu da shaye-shaye.

Ya kuma yaba wa Gidauniyar Bintu Aliyu bisa ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da wannan mugunyar halayya da ke gurgunta makomar matasa, da basu tallafin inganta rayuwarsu.

ƙungiyar ta raba wasu magunguna da ake bai wa masu shaye-shaye, don ya wanke musu huhu daga ɗaukar sinadaren da suke zuƙa na taba da wiwi.

An gudanar da wannan taro ne a tsakiyar unguwar Congo-Rosha, wani yanki da ya yi ƙaurin suna wajen harkar shaye-shaye da baɗala iri-iri, a tsakanin matasan Musulmi da Kirista, da ke haɗuwa suna cin karensu babu babbaka.

Taron ya samu halartar Mai Unguwar yankin, da Shugaban Matasa, da suka bayyana jin daɗinsu da faɗakarwar da aka yi musu, wacce suka yi alƙawarin isar da saƙon ga sauran matasa da suke cikin wannan unguwa.

By ukarofi