Girmama matasa da ba su dama zai kawo ci gaban Nijeriya – Farfesa Adamu Tanko

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Mataimakin Shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya ce akwai buƙatar dattawan Nijeriya, da shugabanin Nijeriya, kowa ya yi karatun tanutsu ta hanyar cewa wannan ba zamaninka ba ne ka bar wa yara matasa ka zama uba malami mai karantarwa da shawarwari ga matasa kamar yadda shugabar ƙasar Naizland, ta sauka da kanta, ya ce wani ya riƙe qasar ta yi iya nata ƙoƙarin, saboda kishin al’umma da ƙasar ta a lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar jami’ar dake birnin Kano a wannan lokaci.

Haka kuma ya ce, “baiwar matasan Nijeriya, ɗimbin basirar da Allah ya yi wa miliyoyin matasan Nijeriya, masu sana’ar gyaran waya, da kwamfuta da dangoginta da duk wani abu da ya shafi waya, a wannan zamani da irin miliyoyin matasa da Allah ya albarkaci Nijeriya, da shugabanninmu na da basirar gano wannan ni’ima da Allah ya yi wa Nijeriya da guraban aiki a Nijeriya sai ya yi kaɗan.

“Amma daskarewar basirar, shugabanni ta haddasa rashin fahimtar muhimmancin cewa sana’ar gyaran waya, da dangoginta aiki ne muhimmi da gwamnati za ta karɓa ta inganta shi ta sabunta shi ta horar da matasa ta taimaka musu ta sa su a hanya, haka matasa masu fim da waƙoƙi da ƙirƙire-ƙirƙire da matasan Nijeriya ke yi, wannan babban jari ne ga gwamnatin Nijeriya da al’ummarta baki ɗaya.”

Mataimakin Shugaban Jami’ar ta Baba Ahmad dake Kano na tare da jami’ansa da suka haɗa da Samuel O, sai magatakardar jami’ar Mr Shuaibu Inuwa Mora, sai kuma jami’ar yaɗa labarai ta jami’ar Hajiya Maryam Sani Gano wanda suka kasance tare da Farfesa Tanko.

Shehun malamin jami’ar, Adamu Idris Tanko, ya ce “abinda matasa suke buqata shi ne ilimi, da kyakyawan jagoranci na shugabancin kishin al’umma da qasa domin a cewarsa a yau waɗancan matasa ‘yan fim, da masu sana’ar waya in ka ce ka rufe kasuwar sayar da waya da gyaranta ko ka hana fim zai zama abu mai wahala a zauna lafiya a ƙasa, don haka mai ya kamata shugabanni su yi ?

“Saboda haka abin yi sai ka karva ka gyara ka inganta abinda ba daidai ba ka kawar da shi a wannan harka dama duk wani aiki da matasa ke yi ba daidai ba.”

ya ƙara da cewa “amma rashin ilimi matsala ce babba domin ilimi kamar ruwan sama ne ga matasa da ƙananan yara dole ka ba su ilimi in ko ba ka ba su ba to ilimi zai ambaliya daga matasan domin za su samu ilimin yau da kullum wanda kuma in ya yi ambaliya tamkar ambaliyar ruwan sama an sai dai abinda ambaliya ke haifarwa a ƙasa.”

A ƙarshe ya ce, “akwai wata matsala da ta faru a ƙasar nan ita ce ta yajin aikin jami’o’i na wata takwas wanda wannan babbar illa ce wacce ba za a gane mummunar ilar da yajin aikin rufe jami`o’in Nijeriya ya jawo ba sai nan gaba, muddin ba a ɗauki mataki na gaggawa wajen magance wannan matsala ba, to sai a nan gaba za a ganta kuma wannan ya faru a fannin gudanar da aikin gwamnatin Nijeriya, musammam lokutan da aka ɗauka ba a ɗaukar ma’aikata da a ka zo wani mataki bayan ɗan lokaci kaɗan an ga illarsa takunkumin ɗaukar ma’aikata a gwamnatance tun da abu ne a tsare waɗannan su yi ritaya waɗanan a ɗauke su aiki haka tsarin ya ke a ilimance da aikace a gwamatance.”