Gobe Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS za ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS mai zaman kanta dake garin Keffi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Mohammad Idris Lukumbogo ya ce a ƙoƙarinta na cigaba da samar wa al’ummar jihar da qasa baki ɗaya ingantataccen ilimin kiwon lafiya na zamani, Kwalejin ta FAMSAS ta kimtsa caf don gudanar da wani gagarumin taron ta mai muhimmanci mai kuma ɗimbin tarihi wato na rantsar da sabbin ɗalibanta da suka samu damar fara karatu a kwalejin na zangon karatun shekarar 2023 da ake ciki a gobe Asabar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2023 da ake ciki.

Cikin wata takardar sanarwa ta musamman wadda shugaban ya sanya hannu, wakilin Manhaja ya samu kwafi, ya sanar cewa sabbin ɗaliban za su ɗauki rantsuwar kasancewa ɗalibai kuma jakadun kwalejin ne nagari kuma za su yi karatu ne a wasu kwasa-kwasan kwalejin daban-daban da suka haɗa da Community Health da Medical Laboratory Science da Health Information da Biostatistics da sauransu.

Alhaji Mohammed Idris Lukumbogo ya kuma bayyana cewa duka waɗannan kwasa-kwasai da sauransu da dama da kwalejin ke gudanarwa a yanzu dukkansu hukumar dake sa ido a harkokin kwasa-kwasan manyan makarantu na gwamnatin tarayya tuni ta amince ta kuma tabbatar da su cikin doka. Kuma a cewarsa kwalejin tana gudanar da waɗannan kwasa-kwasan ne da manufar agaza wa ƙoƙarin gwamnatin jihar ta Nasarawa da na tarayya baki ɗaya ke yi na inganta yanayin kiwon lafiyar al’umma baki ɗaya, don idan aka bar wa gwamnatocin kaɗai ba za su iya sauke nauyin ba.

Har ila yau shugaban kwalejin nazarin kimiyyar lafiyar ta FAMSAS Alhaji Mohammed Idris Lukumbobo ya yi amfani da damar inda ya sanar cewa kawo yanzu daga cikin ɗimbin nasarori da kwalejin ta cimma sun haɗa da na haɗin gwiwa tsakaninta da sauran hukumomin gwamnatin jihar da waɗanda ke zaman kansu, inda sukan turo ɗalibansu waɗannan wurare don ƙarin ilimi da sanin makamar aiki da sauransu.

Daga nan sai Lukumbogo ya kuma yi amfani da damar inda ya tunatar da sabbin ɗaliban da kuma iyayensu da waɗanda aka gayyatasu tabbatar sun hallara kuma cikin lokaci a goben, sannan su kasance masu bin dokokin bikin ɗaukar rantsuwar kamar yadda aka san ɗaliban kwalejin da shi da daɗewa.