Hukumar Alhazan Jihar Kano ta soma bitar mako-mako ga maniyyata

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙaddamar da fara gudanar da bitar mako-mako ga maniyyatan aikin Hajjin bana.

Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishinan ayyuka na musamman, Hon. Kabir Muhammad Tarauni da ya wakilci Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce irin kulawa da Gwamnan Kano ke bai wa cigaban addini ya sa ake tsara bitar da wuri.

Ya ce bitar ta ilmantar da da maniyyata ne dukkan nauyi da ya ɗoru a kan su na ibada da za su aiwatar don kyautata aikin Hajji da za su je.

Kabiru Muhammad Tarauni ya yi kira ga maniyyatan su sanya Jihar Kano da ƙasar nan baki ɗaya a cikin addu’o’i don samun cigaban zaman lafiya da yalwar arziƙi.

Shi ma tun da farko a jawabin sa na maraba, shugaban hukumar Alhazai na Kano, Farfesa Sheikh Abdullahi Pakistan ya yaba da irin gudumnuwa da kulawa da Gwamna Ganduje yake bai wa aikin Hajji.

Sheikh Pakistan ya ce Jihar Kano a bana tana da Alhazai sama da da 5,000 da aka sahale mata, kuma Alhazan da ba su samu tashi a bara ba, su ne za su zama farkon tashi a karon.

Shi ma a nasa jawabin babban sakataren hukumar jin daɗin Alhazai na Jihar Kano, Ambasada Muhammad Abba Ɗanbatta, ya ce bayan gabatar da rahoton aikin Hajjin bara ga Gwamnan Kano sai ya bada umurnin a shiga shirye-shiryen aikin na bana.

Ɗanbatta ya ce hauhawar da ake samu na kuɗin Hajji na faruwa ne saboda tashin Dala. Gwamnatin jihar ta yi kyakkyawan tsare-tsare don tabbatar da nasarar aikin Hajjin na bana.

Shi ma babban kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Ibn Sinah ya ce wannan bita na mako-mako na daga cikin tsare-tsaren bitoci da za su riƙa gabatarwa tun daga shirye-shiryen tafiya har dawowa.

Taron ya samu halartar wakilin shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na qasa na shiyyar Arewa maso Yamma, da na hukumar shige da fice da na NDLEA da Kwastom da NOA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *