Ambaliya ta jawo asarar biliyan 700 a harkar noma – Rahoto

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani rahoto da hukumar faɗaɗa harkar noma da bincike (NAERLS) ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa a Nijeriya ta lamushe Naira biliyan 700 na kuɗin da aka zuba a harkar noma a ƙasar.

A yayin da yake miƙa wannan sakamakon rahoton ga Ministan Noma da raya karkara, Daraktan zartaswa na NAERLS, Farfesa Emmanuel Ikani ya bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta lalata filayen noma, ta lalata amfanin gona abinda ya jawo ƙarancin amfanin gonar da kuma asara ga manoma.

Ya ƙara da cewa, bincike ya nuna cewa, an samu zaizayar ƙasa a wurare fiye da 300 a jihohi 10 da suka fi tavuwa a Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Yammacin Nijeriya.
Haka yawan shan ruwan da ƙasar ta yi shi ma ya taimaka wajen lalata ƙasar da hana ta yin abin arziki a noma. Abinda zai jawo naƙasu a harkar noma da kiwo na tsahon lokaci, a cewar sa.

A taƙaice dai a cewar sa, darajar abinda aka rasa a sakamakon ambaliyar 2022 ya kai na Naira biliyan 700.

Sannan bugu da ƙari a cewar sa, ba a nan asarar kaɗai ta tsaya ba. Ambaliyar a cewar sa ta kuma lalata hanyoyi da gadoji da sauran hanyoyin sufuri. Hakan ya sa manoma sun kasa yin sufurin kayan gonarsu zuwa kasuwanin da za su kai. Haka ambaliyar ta lalata ɗakunan ajiyar amfanin gonar.

Hakazalika kuma a cewar sa, har ma a kan alumma wannan ambaliya ta yi aikinta na cutarwa. Inda a cewarsa mutane da dama sun mutu, wasu sun raunata, wasu kuma sun vace, yayin da kuma wasu suka kamu kuma sun yaɗa cututtukan da akan samu a dalilin gurvatar ruwa da muhalli.

A shekarar 2022, a garuruwan Borno, Adamawa, da Yobe kaɗai an samu vullar cutar kwalara inda aka samu kesa-kesai 586,110 da 320, kuma kusan mutane 300 ne suka mutu a sakamakon haka.

Daga ƙarshe, Farfesa ya yi kira ga ‘yan Nijeriya mazauna waɗancan yankunan da kuma gwamnati a kan su haɗa hannu don kiyaye afkuwar ambaliya a nan gaba.