Rashford ne ɗan wasa mafi cin ƙwallaye tun bayan kammala gasar kofin duniya – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani rahoto da Sport Lite ta fitar ya nuna cewa, bayan wasan Manchester United ta tashi 2-2 da Leeds United a kwantan gasar Firimiya ranar Laraba a Old Trafford, cikin waɗanda suka ci wa Man United ƙwallo har da Marcus Rashford, wanda ya zura na 20 a dukkan fafatawa a bana.

Haka kuma ɗan ƙwallon tawagar Ingila ya ci na 12 kenan tun bayan da aka kammala gasar kofin duniya a Qatar.

Rashford mai shekara 25 ya ci ƙwallo na shida a jere a Old Trafford a Firimiya, bayan Wayne Rooney mai takwas a tsakanin Afirilun 2012.

Ɗan wasan tawagar Ingila ya fara cin ƙwallo ana gama gasar kofin duniya ranar Laraba 21 ga watan Disambar 2022 a Carabao Cup da United ta ci Burnley 2-0.

Rashford ya zura takwas a raga a Premier da uku a Carabao Cup da ɗaya a FA Cup, tun bayan da aka gama gasar kofin duniya a Qatar.

United ta ci gaba da zama a mataki na uku a teburin Firimiya mai maki 43 da tazarar biyu tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Arsenal ce ke jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan da maki 50.

Ranar Lahadi United za ta ziyarci Elland Road, domin buga wasa na biyu a Premier League da Leeds United.

Ranar Litinin leeds ta kori Jesse Marsch, wanda ya ja ragamar ƙungiyar ƙasa da shekara ɗaya.

Bayan da Leeds ta tashi 2-2 da United a Old Trafford ta koma ta 16 daga mataki na 17 da makinta 19.