Majalisar Ƙasa ta amince da sake fasalin Naira

Spread the love

*Ta buƙaci CBN ya ba da himma wajen samar da wadatattun sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Ƙasa ta amince da sake fasalin takardun Naira na 200, 500 da kuma 1000 da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi.

Majalisar ta nuna amincewarta ne yayin zaman da ta yi ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ta kuma shawarci CBN da ya ba da himma wajen aiwatar da sabbin tsare-rsarensa domin rage wa ‘yan ƙasa wahalar ƙarancin kuɗi da suke fuskanta.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan taron, Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce Majalisar ta karɓi bayanai daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda dangane da zaɓe mai ƙaratowa.

A cewar Malami, “Manyan dalilai biyu ne suka haifar da zaman; dalilin farko shi ne game da sha’anin zaɓe wanda a iya cewa ana kan turbar da ta dace duba da nasarar da INEC ta cim ma a shirye-shiryenta.

“Na biyu, shi ne game da sake fasalin Naira, matakin ya yi, sai dai Majalisar ta ce akwai buƙatar CBN ya ba da himma wajen aiwatarwa musamman samar da sabbin kuɗin a wadace.”

By Editor