Shugaba Buhari ya yi alƙawarin mutunta umarnin kotu don cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai mutunta umarnin da Kotun Ƙolin ƙasar ta bayar a kan ƙarar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

Gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar ƙarar inda suke ƙalubalantar wa’adin.

Da sabon ci gaban da aka samu, ’gan Nijeriya na da damar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu su yi amfani da tsoffin takardar kuɗin Naira

Sai dai ya bayyana cewa, gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace don yin watsi da dokar ta wucin gadi.

Malami ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na ARISE News TV.

Kotun ƙolin ta yanke hukuncin ne a ranar Larabar da ta gabata, ta dakatar da wa’adin da babban bankin na CBN ya ke yi na yin tuhume-tuhume tare da sanya ranar 15 ga watan Fabrairu domin sauraren wannan batu.

Malami ya fayyace cewa, gwamnatin tarayya, bisa la’akari da bin doka da oda, za ta bi umarnin kotun ƙoli, duk da cewa tana da niyyar ƙalubalantarta kuma za ta yi hakan ne a cikin tanadin doka.

By Editor