Daga WAKILINMU
Limamin Masallacin Makka, Sheik Saud bin Ibrahim Shuraim ya yi murabus daga muƙaminsa.
Limamin ya ba da uzurin sake sabunta kwantiraginsa da Fadar Shugaban Ƙasa a ƙarshen watannin 2022 bisa dalilan kansa.
Bayanai sun ce limamin zai iya zuwa ya jagoranci Sallar Tarawi wadda za a tabbatar da shi kafin Ramadan mai zuwa.
Majiyoyi sun ce limamin na da damar sabunta kwantiraginsa a kowane lokaci sannan ya koma kan matsayinsa.
Sai dai babu wani bayani a hukumance daga shugabancin kula da Masallattan Makka da Madina da ke tabbatar da murabus ɗin da Sheikh Shuraim ya yi.
Haka nan, ba a jiyo Fadar Shugaban Ƙasa ta ce komai game da haka ba.