Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gurfanar da Rashida, matar Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa zargin zamba.
Har ila yau, a ranar Larabar an gurfanar da Ali Bello a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ke a matsayin ƙani ga gwamnan Kogi.
A cikin wata sanarwa da Wilson Uwujaren, kakakin hukumar EFCC ya fitar, hukumar ta ce an tsare mutanen biyu ne tare da wasu mutane uku bisa tuhume-tuhume 18 da ake yi musu na “vangare da almundahana da kuɗaɗe har Naira biliyan 3,081,804,654.
“Kai Ali Bello, Abba Adaudu Rashida Bello (gaba ɗaya) a wani lokaci a cikin watan Nuwamba 2021 a Abuja a ƙarƙashin ikon wannan kotun mai girma ta hanyar kamfanin E-Traders International Limited an miqa jimillar kuɗi $570,330 zuwa lambar asusu; 426-6644272 da ke a bankin TD, Amurka, wanda a taqaice ya kamata ku san nau’ikan wani ɓangare na kuɗaɗen haram da almubazzaranci da laifuka, kuma kuka aikata laifin ya sava wa sashe na 15(2)(d) na Dokar Hana Halartar Kuɗi, 2011 kamar yadda aka yi mata gyara kuma ta zartar da hukunci a ƙarƙashin sashe na 15 (3) na wannan dokar.”
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Rotimi Oyedepo, lauyan EFCC, ya roƙi kotun da ta sanya ranar shari’a, amma lauyan da ke kare Ahmed Raji ya buƙaci a bayar da belinsa kafin lokacin da za a tantance ƙarar.
Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake qara a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan neman belinsu.
An kuma ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu.
