Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad ya bai wa al’ummar Dambam tabbacin masarauta matuqar suka sake ba shi damar mulki wa’adi na biyu a wannan zaɓe dake tafe.
“Idan ɗaukacin ku, kuka jefa min mafi yawan ƙuri’o’inku waɗanda a fayyace za su zarta mafi yawan ƙuri’o’i da zan samu a ƙaramar hukumata ta Alkaleri a zaɓen ranar 11 ga watan Maris, kuna da tabbacin cewa zan ƙirƙiro maku masarautar sarki mai daraja ta biyu a garin Dambam,” Gwamna ya shaidar masu.
Gwamna Bala Mohammed ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da tawagar yaqin neman zaɓensa ta ziyarci Dambam a kwanakin baya yayin da ya shiga zango na biyu na tsakiyar mazaɓar Sanata ta Bauchi ta Tsakiya, da ta ƙunshi qananan hukumomi shida na Dambam, Misau, Darazo, Ningi, Warji da Ganjuwa, wuraren da ya samu tarba da cincirindon jama’a.
Mohammed, wanda ya lasafta yawan ayyukan cigaba da ya aiwatar wa al’ummomin ƙaramar hukumar Dambam a lokacin ziyarar, ya kuma lura da cewar, a ce gwamnatinsa ta samu nasabar mulki a sama kamar a majalisun Dattawa da ta Wakilai, da romon dimukuraɗiyyar da jama’ar Dambam za su sharɓa zai wuce misali a wannan zangon mulkin siyasa da ake ciki.
Gwamna sai ya buƙaci jama’ar Dambam da su ɗabbakar Jam’iyyar PDP a dukkan matakan zaɓe daga sama zuwa ƙasa domin dacewa da bunƙasar tattalin arziki, ƙarfafa matasa da mata, da kuma cigaba da sharɓar romon dimukuraɗiyya.
Ya bayyana cewar, jama’ar ƙaramar hukumar Dambam a kowane lokaci suna cikin zuciyarsa, kamar yadda tallafe-tallafen da yake yi masu ke nunawa, ya ƙara da faɗin “Dambam da Misau duk da la’akarin cewa suna nesa da fadar jiha, amma gwaraza ne a cikin tafiyar Jam’iyyar PDP da gwamnatinta.
“Dambam da Misau suna da nasabar makamancin tarihi da suke da jinsi daban-daban da suka haɗa da Fulatanci, Barbanci da kare-karenci. Waɗannan al’ummai sun nuna halaccincu a shekarar zaɓe ta 2019 yayin da ɗaukacin suka ɗabbaka wa Jam’iyyar PDP, duk da cewar, ba su da wakilai a majalisun jiha da ta tarayya, dangane da haka ne ma ya sanya nake wakiltarsu a dukkan matakan mulki ba tare da gajiyawa ba.
Ƙauran na Bauchi ya shaida wa cincirondon jama’a da suka yi tsinke wa filin ƙwallo na garin Dambam, inda ake gabatar da lakcocin neman zaɓe cewar, ko da suna yi masa riƙon agola ne, ya taka rawar gani wajen samar da abubuwan more rayuwa wa jama’ar Dambam, musamman a fannonin kiwon lafiya, ruwan sha, ilimi, hanya da makamantansu, tare da yin alƙawarin cigaba da tagazawa a dukkan tsawon mulkinsa.
Gwamna Bala Mohammed sai ya nemi jama’ar Dambam da su kaɗa kuri’o’insu wa Shettima, Bappah Aliyu da Abdul Ahmed Ningi da suka tsaya takara a majalisun jiha, tarayya da ta Dattawa, kana su zaɓi Gwamna Bala Mohammed ya ƙarasa ragowar shekarunsa huɗu akan karagar mulki, haɗi da uwa-uba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa mai kama ragamar mulki a watan Mayu mai gabatowa, yana mai cewa a dunƙulensu za su gudanar wa jama’a ayyukan cigaba.
Mohammed ya bayyana cewar, Atiku Abubakar shi ne mafi ƙwarewa a shugabancin Nijeriya a ire-iren waɗannan halaye na koma-baya da ƙasar take ciki, kamar yadda rawar da ya taka a baya ke gaskata buƙatar shugabancinsa.
Ya kuma bayyana cewar, duk da PDP tana matsayin abokiyar adawa a gwamnatin tsakiya da kuma maras rinjaye a majalisar jihar Bauchi, gwamnatinsa ta yi rawar gani wajen aiwatar da ayyukan cigaba, musamman idan an yi la’akari da yadda ta gina cibiyoyin kiwon lafiya fiye da dubu ɗaya a cikin sassan jiha, haɗi da samar da makarantu barkatai, gina hanyoyin sufuri da ƙarfafa marasa ƙarfi, husasan matasa da mata a ɗaukacin faɗin Jihar Bauchi.
