Gobara ta kama otal ɗin da mahajjatan Nijeriya 480 suke a Makkah

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gobara ta kama wani sashi na Otal ɗin Imaratu Sanan, wanda ke ɗauke da mahajjatan Nijeriya guda 480 a birnin Makkah.

Otal ɗin yana wani yanki ne da ake kira da Sharamansur a ƙasar Mai Tsarki.

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta tabbatar da cewa baki ɗaya mahajjatan 480 suna nan cikin ƙoshin lafiya.

A sanarwar da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce agajin gaggawa daga hukumomin Saudiyya da hukumar gudanarwar otal ɗin sun taimaka wajen kashe gobarar cikin ƙaramin lokacin gabannin ta mamaye sauran sassan ginin gidan.

Akan haka ne, Shugaban NAHCON, Farfesa Sale Abdullahi Usman tare da wasu manyan jami’an hukumar suka garzaya wajen da abin ya faru domin duba matakin al’amarin da ɗaukar matakan da suka dace.

By Babaji