An fusata da yafiya ga fursunoni 11 da gwamnan Neja ya yi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata ƙungiya mai suna Gaba Development Association daga Ƙaramar Hukumar Lavun a Jihar Neja, ta bayyana rashin gamsuwarta da yafiya ga fursunoni guda 11 da ke da hukuncin kisa akansu da Alƙali Maimuna A. Abubakar ta Babbar Kotun jihar ta yi musu, waɗanda aka tsare bisa laifin kisan mutane bakwai a Ƙauyen Gaba.

Shugaban ƙungiyar, Mista Paul Gana a yayin taron manema labarai a Minna, ya roƙi Gwamna Umar Bago na jihar da ya janye batun yafiyar, inda ya ce hakan ya sosa wa iyalan waɗanda aka kashe zuciya.

Ya ce, a shekara 2018 ne aka kashe mutane bakwan a lokacin da suke tsaka da ayyuka a gonakinsu da kuma raunata wasu guda biyu.

Ya bayyana cewa, tsawon shekaru huɗu al’ummar ƙauyen suka shafe suna neman a yi musu adalci, inda a shekarar 2022 aka yanke wa masu laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ya ƙara da cewa, babu zama na neman zaman lafiya ko ɗaya da gwamnatin ta shirya wanda al’ummar ƙauyen suka samu wakilci a ciki, lamarin da ke nuna cewa ba su amince ba.

Mista Gana ya kuma yi gargaɗin cewa, yafiyar ka iya zama barazana ga zaman lafiyar al’ummar ƙauyen da yankunan da ke kewaye da shi.

Masu laifin da aka yi wa yafiyar sune: Mohammed Mohammed, Ndana Alhaji Sheshi, Isah Baba Madu, Mohammed Mohammed Nda Bida, Abubakar Baba Salihu, Baba Mohammed Shaba, Adamu Mohammed Baba, Haruna Muhammed, Isah Mohammed Alhaji Inuwa, Ibrahim Mohammed, da kuma Mohammed Isah.

By Babaji