Nan da mako biyu haɗakar jam’iyyu za su fidda matsaya kan tafiyarsu – Mustapha Inuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Nan da mako biyu masu zuwa haɗakan jam’iyyu a ƙasar nan zasu fidda matsaya kan tafiyar su.

Dr Mustapha Muhammad Inuwa, ɗaya daga cikin jigajigan haɗaka ya faɗi haka a Katsina lokacin da yake wa ɗunbin magoya bayan haɗakan a ofishin sa.

Ya ce tafiya tayi nisa wajen shiryar shiryen haɗewa waje ɗaya domin tunkara zaɓe mai zuwa.

Dakta Mustapha Inuwa wanda yake shugabantar tsagin jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ya bayyana cewa suna yi suna taka tsantsan ganin yadda jam’iyyar adawa ta PDP ta tasar ma rugujewa a ƙasar.

“Shi yasa muke taka tsantsan domin kada mu faɗa irin wannan yanayi na karya yan adawa da wannan gwamnati ke yi,”inji Mustapha Inuwa.

Ya kuma gargaɗi ya’yan gamayyar jam’iyyun da su guji kawo banbance banbance a wannan tafiya.

Dakta Mustapha Inuwa ya kuma nuna takaicin sa ga yadda gwamnati APC ta jefa al’ummar ƙasan cikin talauci da rashin tsaro.

Yace dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye wajan kawar da wannan gwamnati ta hanyar kafa irin wannan haɗaka.

Shima ɗan kwamitin zartaswa na haɗakan sanata Ahmed Babba Kaita ya ce ana ta tattaunawa da ya’yan jam’iyyun adawa harda wasu jigajigan jami’ar PDP wajen sabon ganin an haɗe.

By ukarofi