Gobara ta lalata kayan ma’aikata a gidan rediyon Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wata gobara ta tashi a harabar gidan rediyon Gombe wato Gombe Media Corporation (GMC), inda ta lalata wasu sassa na kamfanin tare da ƙone kayayyaki da wasu kadarorin ma’aikata da masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) da ke aiki a wurin.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:50 na yammacin Asabar, inda ta shafi tsohon ɗakin shirya shirye-shiryen talabijin, sashen kula da na’urori, ɗakin adana kayan rediyo, ofishin daraktan labarai da kuma masaukin ’yan NYSC da ke aikin GMC Radio da Television.

Da samun labarin gobarar, jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Gombe da ta tarayya sun isa wurin, inda suka yi ƙoƙarin kashe ta tare da hana ta bazuwa zuwa sauran sassan harabar.

Daraktan Janar na GMC, Malam Ibrahim Isa, shi ma ya isa wurin tare da daraktan janar na yaɗa labarai na gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, da ma’aikatan gidan rediyo da talabijin ɗin da sauran jama’a domin duba halin da ake ciki.

Ba a samu asarar rai ba sakamakon gobarar, sai dai wasu mutane sun samu ƙananan raunuka yayin da suke ƙoƙarin ceto kayayyaki da taimakawa wajen shawo kan lamarin.

Da yake magana a wurin da lamarin ya faru, daraktan janar na GMC, Ibrahim Isa, ya bayyana gobarar a matsayin abin takaici, yana mai godiya ga Allah da ba a rasa rai ba.

Wasu daga cikin ’yan NYSC da lamarin ya shafa, Farida Tahir, Esther Daniel da Nasiru Joshua, sun ce gobarar ta lalata musu muhimman kayayyaki, ciki har da kwamfutocin tafi-da-gidanka, ke ƙunan ɗinki da wasu muhimman takardu.

Haka kuma, wani mai ɗaukar hotunan talabijin kuma mai zanen sashen labarai na GMC, Irmiya Maiguwa, na daga cikin waɗanda suka samu ƙananan raunuka yayin da yake ƙoƙarin taimakawa wajen kashe gobarar da kuma ceto kadarorin da ke cikin wurin.

Lamarin ya janyo hankalin ma’aikata da jama’a da dama zuwa harabar gidan rediyon, yayin da jami’an kashe gobara suka ci gaba da aikin tabbatar da cewa an shawo kan gobarar gaba ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply