Gobara ta tashi sau 15 a jere a unguwar Danbare a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wata mata mai suna Hajiya Hauwa Mai-kitso da ke zaune a unguwar Danbare B da ke Ƙaramar Hukumar Kumɓotso a Jihar Kano ta koka akan yadda gobara ta addabe ta.

Gobarar wacce ya zuwa yanzu ba a san daga ina matsalar ta ke ba, amma al’umma sun fara hasashen cewa ko aljanin nan mai suna Batoyi ne ke haɗa mata gobarar, duba da cewa wutar ce ka tashi ba tare da wani musabbabi ba.

A zantawarsa da manema labarai Hajiya Hauwa ta ce sau goma sha biyar kenan wutar na tashi, inda ta ce ko ta kai kayan nata wani gida, sai wutar ta bi su can ta ƙone su.

A cewar ta, ta yi iya bakin ƙoƙarin ta, kuma gashi duk kuɗaɗen ta da kayan ta sun ƙare.

Cikin alhini da damuwa, Hajiya Hauwa ta ce ” Ina da marayu ina tare Ni nake kula da su kayan su duk sun ƙone. Koma irin kwancen kayan nan da al’ummar Annabi su ke taimaka mana da su, su ma sai ƙone wa su ke yi

“Na rasa inda zan saka kai na kuma ana ta yin addu’a ko Talatar da ta wuce anyi karatun Alƙur’ni da addu’oi, Wasu sun ce ko aljanin Batoyi ne, to ni dai Allah ne masani.

“Ina dai rokon taimakon al’umma da a kawo min ɗauki dan Allah dan Annabi,” in ji Hajiya Hauwa.

Gobarar wacce ta fi ta shi a ranakun Alhamis, Juma’a, da Asabar, a mafi yawan lokacin kuma tana ta shi ne daga 8 na safe zuwa sha daya na safe. Makotan a unguwa ne dai suke kokarin kashe wutar a duk lokacin da take ta shi.