Gobe Asabar 1 ga Ramadan 1443 – Sarkin Musulmi

Daga AMINU ALHUSSAINI AMANAWA a Sokoto

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bada sanarwar ganin jinjirin watan Ramadan na Shekarar 1443 a sassan ƙasar nan.

Sarkin ya bayyana cewa, Sun samu rahoton ganin watan Ramadan daga shugabanni da kuma ƙungiyoyin addinin Musulunci, tare da tantacewar kwamitin duban wata n’a majalisar.

Mai Martaba Sarkin Musulmi yayi amfani da wannan damar wajen kira ga al’ummar Musulmi da su dage da ibada, tare da aiki da koyarwar addinin Musulunci dama addu’ar samun zaman lafiya a Najeriya bakiɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *