Gidauniyar Bintaliya ta bada tallafin azumi a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne gidauniyar Bintaliya, wata gidauniya da ta yi fice wajen tallafa wa al’umma masu ƙaramin ƙarfi, ta raba wa dubun-dubatar al’umma kayan abincin azumin watan Ramadan a Jihar Kaduna.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna.

Gidauniya ta bayar da irin nata tallafin ga al’umma ne musamman Waɗanda ke buƙatar taimako a garin Kaduna, inda ta ba wa dubun-dubatar al’umma tallafin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, taliya, maggi, Makaroni, gishiri, wanda al’umma da dama su ka amfana.

Wakilinmu da ya shaidi rabon waɗannan kaya, ya shaida mana cewa, ita kanta Shugabar wannan cibiya, Hajiya Binta Hamidu Haruna ce da kanta ta ke jagorantar raba waɗannan kaya tare da ɗaukar matakan da suka dace don ganin an yi rabo cikin aminci.

A zantawar da ta yi da manema labarai, Hajiya Binta Hamidu Haruna ta bayyana cewa, ita tana ganin abu ne mai muhimmnanci a taimaka wa waɗanda ba su da shi, musamman a wannan lokaci da jama’a ke cikin mawuyancin hali na rashi.

Ta ce, “a yanzu babu wanda zai ce ya ƙi taimako, in dai har zai samu, samuwarsa shi ke da wuya a yanzu, muna fatan waɗanda su ke da hali za su taimaka, kuma ita gwamnati da ta ke taimaka wa Ƙungiyoyi, za ta dube mu mu ma ta taimaka mana don mu ma mu taimaka wa jama’a, don mun fi kusa da jama’a, kuma mun saba muna yi, kuma saboda dama ba ta tada yi mana komai ba. Duk abin da aka ba mu, za mu bayar da shi ne ga mabuƙata.”

Hajiya Binta ta ci gaba da bayyana cewa, “daidai gwargwadon abin da Allah ya ba ni da kuma masoya da suke tare da mu, su ma suna ba da tallafin su, da kuma ‘yan uwa waɗanda suke kasuwanci, su ma suna kawo taimakonsu, Alhamdu lillah! Da shi al’umma ta ke amfana, babu abin da za mu ce sai dai godiya.”

Daga nan sai Bintaliya ta yi kira ga waɗanda Allah ya hore ma abin hannu, su fito su taimaka wa jama’a, musamman a wannan lokaci da jama’a ke cikin mawuyacin hali na rashi a azumi ya ƙaratowa.

Ta kuma bayyana cewa, shi wannan tallafi na ilimin kayan abincin azumi ba nan kaɗai ta tsaya ba, tana horar da jama’a da dama ilimin kwamfuta, maza da mata, musamman matasa. Sannan ta na ba da bashi ga ƙananan ƙungiyoyi da masu ƙaramin ƙarfi.