“Darul Islam ke da alhaki harin jirgin ƙasa”

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD

A Janairun bara, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa, wata ƙungiya Ansarul Islam, wadda ke da kamanceceniya da Ƙungiyar Boko Haram sun kafa ƙungiyoyi a jihar.

Ya ce, “da yawan mambobin ƙungiyar Darul Islam da ke da alaƙa da Boko Haram ɗin, a yanzu sun karkasu wurare biyar a cikin ƙananan hukumomi 13 da ke yankin.

“Yankunan sune: Nasarawa, Awe, Doma, Wamba da kuma yankin Karu. Wanda ya haddasa matsalar tsaro a jihar kamar yadda ake samun sabbin hare-hare bayan da jami’an tsaro suka fatattake su kwanan nan.”

Haka zalika, yayin da jami’an sojojin Nijeriya suka fatattake su, sun kama sama da mata da ƙananan yara 778.
Mataimakin Gwamnan jihar, Dr.

Emmanuel Akabe, ya ce jihar na ƙoƙarin ganin ta ƙori ‘yan bindiga daga sassan jihar, inda ta samar da muhimman kayan aiki ga sojoji, ya ce ‘yan bindigar su miqa wuya domin su samu su cigaba da harkokin su a cikin jama’a.

“Idan babu zaman lafiya, babu yadda za a yi cigaba ya samu. Nijeriya na buƙatar cigaba. Idan babu zaman lafiya, ba cigaba,” a cewar sa.

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Lolo ya samu wakilcin mataimakinsa, Ahmed Muhammad Ketso a wajen taron.

Jihar Neja ita ke da mafi yawan mutanen da ke hannun ‘yan bindiga, inda mata 86 da yara 232, sannan sai Jihar Kano da ke da maza 20 da mata da ƙananan yara 64.

Jihar Nasarawa na da mata guda takwas da yara 11.

Mata da yara 778 ɗin suna cikin mambobin ƙungiyar Darul Islam da aka tasa a dajin Uttu a Ƙaramar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa satin da ya gabata 

Haka zalika, Rijana, Katari, Gidan Busa duk suna daga cikin ƙauyuka a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da yankin ya zama sansanin ‘yan ta’adda tsawon shekaru.

Wani Mai unguwar ƙauye ya bayyana cewa, “garin Rijana mai kilomita 48 zuwa Kaduna, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Kachia. Ƙabilar Kadara ne suka gina garin, sai kuma yawancin Hausawa da Fulani daga cikinsu.

“Sunan Rijana ya samo asali ne daga rafin Kasuwar Magani da ya yanka ya vulla har Shiroro zuwa kogin Neja.”

A cewarsa, garin yana da firamare da sakandare ne kawai, inda ƙaramar asibitin matakin farko ma ta kasance wajen kwanciyar ‘yan ci-rani.

Majiyar ta ce mazauna garin da kansu suka haɗa kudi suka samar wa jami’an ‘yan sanda da caji ofis. Suna da wata matattar Toyota Hilux da ta yi aƙalla wata shida a ajiye ba a fita sintiri da ita.

Amma motocin da aka samar wa ‘yan sanda da sojoji ana ganin suna aiki da su a babbar hanya.

A kan tsaro, ya ce ƙungiyar ‘yan banga ta bijilante da ke yankin an dakatar da ita saboda jin tsoron yadda ‘yan bindiga ke kai hari fiye da shekara goma yanzu.

Ya ce, lokacin da wasu matasa da ke fama da talauci ‘yan bindiga suka kama su, mutanen garin suna amincewa su kawar da su don kada su yi cuɗanya da ‘yan bindigar. 

Shugaban qauyen ya ce, daga gabas dajin ya haɗu da Kaduna, Zamfara, Kebni har zuwa Jamhuriyar Benin, sai kuma ta  Gabas ya yi mahaɗa da Abuja da Nasarawa da Filato da Bauchi da Gombe da Adamawa har zuwa Kamaru.

Ya bayyana cewa, da daɗewa suna mamakin yadda a ce duk DPO ɗin da aka kai yankin ba ya wuce shekara guda idan aka fahimci yana da ƙoƙari, ka san cewa canja masa wujen aiki ake yi?

Majiyar ya bayyana cewa duk lokacin da wani jami’in tsaro kamar ɗan sanda ko soja ya shiga Rijana, Sabon Gayan, Katari, Gidan Busa, Dutse, da Gada har zuwa Sarkin Fawa a Jihar Neja, gwamnati tana yin wani kuskure na ƙin yin sulhu tsakanin Fulani da makiyaya ko kuma a bisu zuwa mazaunin su ta kawar da su, amma an san duk wuraren da suke.

Hakan na nufin har yanzu ana iya bambance qananan ɓarayi da kuma na gida, ‘yan daba da makamai yanzu Ansarul Islam, masu kama da ‘yan ƙungiyar Boko Haram ɗauke da bom.

Ɓarayin gida su iyakar su satar kaji da kwance kayan mutane, ɓarayi ‘yan tsaka-tsaki kuma su ne garkuwa da mutane da satar dabbobi, amma Ansarul Islam suna tayar da bom.

Haka zalika, wani matashi a garin Gwagwada da ke kusa da sansanin masu bautar ƙasa (NYSC) a Kaduna ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Chikun da yake bayyana damuwarsa, ya ce “sansanin masu bautar ƙasa (NYSC), a yanzu ya tashi daga inda aka saba horas da masu bautar ƙasan ya koma cikin Sakandaren Gwamnati ta Kaduna (GCK), kilomita guda tsakaninta da Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, saboda fargabar kai hare-haren da ‘yan bindiga ke yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wasu daga cikin iyalan ‘yan Darul Salam

“Fiye da ƙauyuka 30 ne suka tarwatse saboda harin ‘yan bindiga ɗauke da gaggan bindigogi ƙirar AK47 suna ta’addancin su kan manoma da makiyaya da sauran al’ummar ƙauyukan.

“Ba zai wuce kilomita 50 ba daga sansanin ‘yan ƙungiyar Darul Islam waɗanda suka hi hijira daga Arewa maso Gabas suka kafa sansani a yankin Sarkin Fawa da ke Ƙaramar Hukumar Munya a Jihar Neja.

“Shawara ɗaya ce ga gwamnati shi ne ta faɗa dajin domin kawar da wasun su da kuma kama wasu don su bayyana sansanonin su tun kafin sun gawurta.

Idan za a iya tunawa, Darul Islam ita ke da alhakin kai hari da jefa bom a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da raunata mutane da dama.

A lokacin lokacin haɗa wannan rahoto, Kamfanonin Jiragen Saman ‘Yan Kasuwa sun soke dukkan tashin jiragen sama zuwa Kaduna saboda rashin tabbas ga tsaron tashoshin jiragen sama yayin da ‘yan bindiga suka kawo tsaiko a tashin jirgi a Kaduna, inda suka kashe ma’aikacin Kula da Zirga-zirga Jiragen Sama (FAAN).