Gobe likitocin Nijeriya za su soma yajin aiki

Daga AISHA ASAS

Likitocin Nijeriya ƙarkashin ƙungiyarsu ta ƙasa, wato National Association of Resident Doctors (NARD), sun yanke shawarar soma yajin aiki a faɗin ƙasa daga ranar Litinin, 2 ga Agustan 2021.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ƙasa ke fuskantar ƙaruwar masu harbuwa da cutar korona, wanda hakan wata babbar alama ce da ke nuni da ɓarkewar annobar karo na uku.

Likitocin sun cim ma matsayar shiga yajin aikin ne biyo bayan taron da shugabannin ƙungiyar na ƙasa (NEC) suka yi wanda ya samu halartar mambaobi sama da 50 a faɗin ƙasa.

Bayanai sun nuna likitocin za su tsunduma yajin aikin ne saboda gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar da suka cim ma bayan sama da kwanaki 100 da suka shuɗe.

Daga cikin buƙatun da likitocin ke buƙatar gwamnati ta magance musu har da batun dakatar da ƙudurin janye jami’ansu na ‘House Officers’ daga tsarin aiki wanda suka ce ba a aiwatar da hakan ba.

Ƙari a kan haka, Shugaban NARD, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, ya ce duk da ƙoƙarin da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi wajen tabbatar da an shigar da kuɗaɗen shirin bai wa likitocin horo cikin ƙarin kasafin ƙasa, amma Gwamnatin Tarayya ta ƙi raba kuɗaɗen ga mabobinsu yadda ya kamata.

Ya ce sun dakatar da yajin aikin kwanaki 113 da suka yi a baya ne saboda alƙauran da gwamnati ta yi musu a yarjejeniyar da aka cim ma a gaban Ministan Ƙwadago, Sen. Dr Chris Ngige.

Likitocin sun kuma koka kan irin baƙar wahalar da suke sha kafin samun albashinsu a tsarin GIFMIS, wanda a cewarsu tsarin na haifar musu da jinkirin samun albashi kama daga watanni uku zuwa bakwai.

Tare da cewa, duk da gwamnati ta yi musu alƙawarin cire su daga tsarin biyan albashi na GIFMIS mai cike da kurakurai zuwa IPPIS, amma har yanzu shuru kake ji, da dai sauran matsalolin da likitocin suka yi ƙorafin an kasa magance musu duk da alƙawarin da aka yi musu a baya.