Yau Dr. Bala Muhammad zai albarkaci taron ƙungiyar ANA a Kano

Daga WAKILINMU

Dakta Bala Muhammad zai halarci taron ANA da ke zuwa duk Lahadin farkon wata, inda zai zo masu da tsarabar ilimi mai taken ‘Iya Magana A Bainar Jama’a’.

Baje kolin fasahar marubuta da ANA Kano kan shirya a duk Lahadin farkon kowane wata zai zo da wata sabuwa ran 1 ga watan Agusta 2021 inda za a gabatar da wani sabon lamari mai taken ‘Gina mutum da koya masa ƙwarewa’, wato ‘Human development and capacity building’ (HD&CB) da zai dinga faruwa a duk wata.

Shin ko ka iya magana a gaban jama’a? Za ka iya yi wa mutane bayani gamsasshe su karɓi ra’ayinka? Ko ka na da sha’awar samun kuɗin shiga ta hanyar yi wa mutane jawabin ilimantarwa har hakan ya zame maka sana’a? To, ga wata dama gwaggwaɓa ta samu.

Dr. Bala Muhammad malami a BUK kuma marubuci a jaridar ‘Daily Trust’, shahararre, gogagge kuma ƙwararren mai iya magana a bainar jama’a ya ƙudiri niyyar koyawa mambobin ANA Kano yadda ake iya yin magana ko jawabi a gaban mutane ba tare da fargaba ko ruɗewa ba.

Wannan sanin makamar aiki a kan kuɗi N150,000 ake koyar da shi, amma Dr. Bala kyauta zai gudanar da shi.

Za a gabatar da wannan bita ne gabannin karatuttukan da aka saba yi duk wata daga rubuce-rubucen marubuta inda daga bisani mahalarta taron kan yi gyararraki, su nemi ƙarin bayani, su ƙalubalanci aikin ko su yi sharhi da dai makamantansu.

Sannan ga masu sha’awar zama ‘yan ƙungiyar ANA Kano mutum zai iya sayan fom don cikewa da hotunansa kai tsaye a wajen taron.

Za a gudanar da taron ne a yau Lahadi,1 Agusta, 2021 a Sakatariyar ANA Kano da ke Ɗakin Karatun Murtala Muhammad, Nassarawa Kano, da misalin ƙarfe 11 na safe.

Waɗannan bayanai sun fito ne ta hannun Sakataren Ƙungiyar, Mazhun Idris.