Goron Juma’a: Matakan kiyaye warin baki ga mai azumi

Daga CHIROMA AMINU ASID

Yana da kyau a bi waɗannan matakai domin samun sauƙin matsalar, kuma kamar yadda na faɗa maku cewa, ba iya rashin yin brush bane ya ke kawo warin baki ga mai azumi. Yana da kyau a kiyaye da abubuwa kamar haka:

1.GOGE HAƘORA DA HARSHE DA KYAU– A tabbata an goge haƙora da makilin mai dauke da sinadarin fluoride bayan an sha ruwa da
bayan sahur don kawar da ragowar abinci da ƙwayoyin cuta da suka maƙale a baki da saman harshe.

2.AMFANI DA ASWAKI – Yin aswaki yana taimakawa wajen kashe ƙwayoyin cuta kuma yana inganta tsaftar baki musamman idan an yi amfani da shi a rana.

3.SHAN ISASSHEN RUWA – Shan ruwa mai yawa lokacin sahur da buda baki yana rage bushewar baki, wanda ke hana wari.

4.TSAFTACE HANCI DA MAƘOGARO– Wanke hanci da kuskure baki da ruwa yana taimakawa wajen cire yawan ƙwayoyin cuta masu haddasa wari.

5.CIN ABINCI MARA SUGAR SOSSAI – Yawan cin kayan zaƙi yana ba da damar haɓakar ƙwayoyin cuta a baki, wanda ke haddasa wari.

6.GOGE BAKI DA SAMAN HARSHE (Tongue Scraper) – Harshen mutum yana tara ƙwayoyin cuta ta hanyar ba miliyoyin ƙwayoyin cuta mafaka da ragowar abinci, don haka yana da kyau a tsaftace shi ko a kankare samansa da kyau domin fitar da duk ɓurɓushin abincin da ya makale acikin saman harshen bayan sahur.

7.GUJE WA CIN ABINCI MAI ƘAMSHI MAI ƘARFI– Abinci kamar albasa da tafarnuwa suna barin wari a baki saboda sinadarin sulfur, don haka yana da kyau a rage yawan cin su kafin a yi sahur.

8.AMFANI DA ANTIBACTERIAL MOUTHWASH– Ana iya amfani da antibacterial mouthwash a kuskure baki kafin sahur domin rage warin baki.

9.GUJE WA SHAN SIGARI – Amfani da sigari ko taba na haddasa wari mai tsanani a baki.

10.GANIN LIKITA IDAN WARIN BAKIN BAI TAFI BA– Idan wari yana da tsanani duk da kiyaye tsafta, yana iya alaƙa da matsalar ciki, haƙori, ko gum ko ulcer saboda haka yana da kyau a ga likita domin bincike.