Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da rufe hanyoyin sadarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da rufe ayyukan sadarwa a wasu sassan jihar saboda ayyukan sojoji na fatattakar ‘yan bindiga a yankunan.

Kwamishinan ya kuma ba da sanarwar haramta amfani da baburan haya na tsawon wata uku daga ranar Alhamis 30 ga Satumba 2021.

A yanzu adaidaita sahu za su fara aiki daga ƙarfe 6 na safe zuwa 7 na yamma yayin da duk motocin haya da ke aiki a jihar za a yi musu fenti da launin rawaya da kore.

Waɗannan da sauran su na cikin matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta zauka tare da shawarar hukumomin tsaro don magance matsalar tsaro a Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Gwamnati ta ce, ta na takaicin irin takurawar da waɗannan matakan za su yi kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, amma sun zama dole ne don cin nasarar yaqi da maƙiyan zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *