`Yan bindiga sun kashe mijin Marigayiya Dora Akunyili

Daga SANI AHMAD GIWA

Wasu `yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yaɗa Labarai, Farfesa Dora Akunyili.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun far masa ne a yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba a Jihar Anambara.

Kodayake zuwa haɗa wannan labari babu wani cikakken bayani daga ɓangaren jami’an tsaro game da al’amarin. Amma wani rahoton Jaridar The Nation ya ce an kashe marigayin ne a Umuoji da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambara da yammacin ranar Talata.

Wata majiya ta kusa da iyalan Marigayin ta ce, marigayin ya halarci taron ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Nijeriya Nsukka (UNAA), inda aka karrama Marigayiya Dora wasu sa’o’i kafin a kashe shi.

A cewar majiyar, “Allah ka mai da shaiɗan da muƙarrabansa marasa marfi da rashin amfani.

“Na kasance tare da wannan mutumin jiya-jiya a Sharon Hall, All Saints Cathedral, Onitsha. Ya kasance a taron Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Jami’ar Nsukka (UNAA), reshen Onitsha, inda suka karrama Marigayiya Dora Akunyili.

Marigayi Dr. Chike Akunyili

“Ya yi magana mai haske game da Dora kuma ya bada gudummawar Naira dubu ɗari 500 ga ƙungiyar. Ya kasance a wajen tare da ɗansa Obum, yanzu yana aiki tare da gwamnatin jihar Anambara.

“Mun raka su wajen motar, kuma ya kasance abin tausayi lokacin da Obum ya rungume shi sosai yayin da su biyun suka rabu don shiga motocinsu mabambanta.

“Obum yana cikin farar Hilux, yayin da mutumin ke cikin babbar Jeep (ina tsammanin Prado). Allah ya jimansa!”