‘Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara

Sarkin Kagara, Alh. Ahmad Garba Gunna

Daga BASHIR ISAH

Bayanan da MANHAJA ta kalato daga Jihar Neja sun nuna ‘yan bindiga sun kai hari a garin Kagara, hedikwatar ƙaramar hukumar Rafi inda suka shiga har fadar masarautar Kagara.

A jiya Talata wannan al’amari ya faru, inda bayanai suka tabbatar da ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan babura da yawansu ya kai 20 inda kowane babur ke ɗauke da mutum uku.

Majiyar jaridar Thisday ta bayyana cewa, an yi sa’a lokacin da aka kai harin Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba Gunna, ba ya gari, ya tafi Minna halartar wani taro.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu labarin hasar rai ko sace wani ko wasu sakamakon harin, amma jami’an tsaro na kan gudanar da bincike.

Yankin Kagara na daga cikin yankunan da suka fi fama da harkokin ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji a jihar Neja, wanda a lokutan baya ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu ɗalibai da dama a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *