Gwamna Abba ya bada tallafin Naira milyan biyu ga makarantar Mu’assasatul Balarabe

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bada tallafin naira milyan biyu ga makarantar Islamiyya ta Mu’assasatul Balarabe Bello Hamza Islamiyya da ke kan titin Sokoto Road cikin birnin Kano.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na mai girma gwamnan ya fitar Malam Usman Gwadabe.

Gwamna ya bada tallafin Kuɗin ne a yayin halartar bikin yaye ɗalibai da sukayi saukar Alqur’ani mai girma da ya gudana a ranar Lahadi.

Da yake jawabi a madadin Gwamnan yayin miƙa tallafin Kuɗin kwamishinan ma’aikatar ilimi na jihar Kano Gwani Haruna Makoɗa ya bayyana irin gwamnan ya ji dadi dangane da wannan ɗalibai.

Makoɗa ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori waɗannan ɗalibai da suka samu damar sauke Alqur’ani mai girma da suyi amfani da abinda suka koya na daga cikin ilimin da tafsirin sa da sauran falalar sa.

Gwamna Abba Yusuf ya kuma miƙa saƙon taya murnar shi ga ɗaliban tare da yi masu nasihar suyi aiki da abinda suka samu damar koyo yayin wannan Karatu tare da basu shawarar su ƙara ƙaimi wajen neman ilimi daban-daban.

Ya kuma baiwa ɗalibai 13 takardar samun shedar kammala saukar Alqur’anin da kammala karatun na wannan lokaci.

A nasa ɓangare shugaban makarantar Mallam Jamilu Yusha’u yace wannan makaranta an sanya mata sunanta ne na bayan yin wafatin marigayi Balarabe Bello Hamza wanda shine kuma ya samar da Makarantar domin samar da horo na musamman na yara bayan sun samu hutun makaranta zasu cigaba da zuwa.

Mallam Jamilu ya yi matuƙar godiya ga gwamna Abba Kabir da yin addu’ar samun rahama ga Marigayi Malam Balarabe Hamza bisa aikin agaza ma al’umma na taimako da ya gabatar.

Shima a nasa jawabin Babban daraktan tsare-tsare da saukar baƙin Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Ibraahim Rogo wanda kuma ya rufe taron da jawabin godiya a madadin iyayen yara da makarantar ya yabama mai girma Gwamna bisa tallafin da ya bayar.

Abdullahi Rogo ya kuma ƙara godiya bisa namijin ƙoƙarin gwamna Abba bisa jajircewa wajen inganta harkokin ilimi a faɗin Kano.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun haɗar da babban daraktan yaɗa labarai na Gwamnan sai Falakin Shinkafi,manyan malamai da dai sauran su.

By ukarofi