Daga RABIU SANUSI
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ƙudurin gwamnatin Kano na cigaba da haɗa hannu da gwamnatin Ƙasar Tunusiya don haɓaka hulɗar Kasuwanci a Jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya Karɓi baƙuncin jakadan Ƙasar Tunusiya a Najeriya Mai Girma Mohsen Antit yayin da yakawo ziyarar aiki fadar gwamnatin Kano tare da muƙarraban shi.
Ziyarar wadda take Ƙara tabbatar da haɗin Kan da ke akwai tsakanin ƙasashen biyu ta fuskar Kasuwanci da kuma take nuni da cigaba da haɗa Kai a tsakani a ɓangarorin da suka haɗa da noma,harkokin da za su samar da cigaba, da harkokin siye da siyarwa.
Gwamnan ya bayyana cewa sanin kowa ne Jihar Kano na matakin gaba wajen bunƙasar tattalin arziki da Kasuwanci tun shekaru masu yawa dan haka dole ta cigaba da riƙe Kambun ta.
Haka kuma Abba Kabir ya kuma bayyana batun samar da fahimta mai ɗorewa da za ta taimaka ga Ƙasar Tunusiya da Jihar Kano,inda ya bayyana Ƙasar matsayin matakin nasara musamman ta fuskar harkokin noma,inda Jihar Kano da Ƙasar Tunusiyan suke da Kambun cigaba a fuskar Kasuwanci.
Haka ma Gwamnan Kano ya kuma Ƙara buƙatar haɗa hannu da Ƙasar ta Tunusiya wajen haɓaka harkokin kawo wasu Kaya na Ƙasar da shigo da wasu kayan amfanin yau da Kullum da kuma inganta kayan rini da jima da ma farfaɗo da guraren da ake gudanar da wannan sana’o’i.
Dangane da hakan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci ma’aikatar kula da zuba jari da ma’aikatar gona da su haɗa wani taro na baje Kolin da waɗannan baƙi zasu gamsu da abinda ake shirin yi don fahimta kan Ƙudurin gwamnatin.
Ya kuma haska batun samar da tashar tsandauri da aka gina matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da zasu taimaka wajen gudanar da Kasuwancin Ƙasa da Ƙasa.
“Ƙananan yan Kasuwa sun shirya fara gudanar da Kasuwanci na shigo da kayayyaki ta wannan tasha wanda kuma muna tsammanin zai ƙara ma Kasuwanci daraja.
Gwamna ya kuma yi alƙawarin samar ma dukkan ƴan Kasuwa da zasu zo Jihar Kano dan Sanya hannun jari,sannan ya kuma nuna godiyar Shi ga wasu mutum 17 daga Kano da suka je Ƙasar Tunusiya dan gudanar da Kasuwanci aka Karɓe su cikin aminchi.
Ya kuma Ƙara baiwa babban manajan daraktan hukumar KAN-INVEST da ya raka waɗannan baƙi zuwa dukkan guraren da Jihar Kano ke alfahari da su wajen Kasuwanci.
Da yake nashi jawabin jakadan na Tunusiya Mohsen Antit ya yaba da irin salon Kasuwancin Jihar Kano da kuma yadda aka Karrama su da tawagar Shi.
Ya kuma Ƙara bada tabbacin cigaba da haɗa Kai da gwamnatin Kano wajen bunƙasar tattalin arziki da inganta Kasuwanci tare da jinjina ma Gwamna Abba da sauran ɓangaren ƴan Kasuwa da sauran ɓangaren gwamnati.
Zaman wanda aka cimma matsaya Kan inganta dangantakar Kasuwanci tsakanin Kano da Ƙasar Tunusiya da zai bada damar haɓaka harkokin Kasuwanci da inganta al’adu.
Wannan na nuni da cewa Jihar Kano na Ƙara samun Karɓuwa ta fuskar Kasuwanci daga ciki da wajen ƙasar Najeriya dama Kasuwancin duniya.
