Gwamna Bala tagomashi ne daga Allah, cewar sarakunan yammacin Afrika

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Babban Sakataren Ƙungiyar Ma’abuta Sarauta ta Yammacin Afirka (Association of West African Monarchs) ‘AWAM’, Kwamred Eliot Afiyo ya bayyana yaƙinin ƙungiyar na cewa Nijeriya za ta kasance kan turba ta ɗaukaka a shekara ta 2023, matuƙar Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kama ragamar shugabancin ta.

Afiyo ya yi wannan furuci ne a birnin Akara ta Ƙasar Ghana a kwanakin baya yayin da yake tofa albarkacin bakin sa a wani taro na ma’abuta mulki da aka gudanar a can ƙasar.

Ya ce, “Masu alfarma, girma, zatuka da abokai. Wata girmamawa ce da aka gayyace ni na bayar da jawabin rufe taro, kamar yadda na yi a wani makamancin sa a garin Ƙuagadogou.

“Za ku iya tunawa ina cikin garin Ƙuagadogou ta ƙassashen Farasanchi makon da ya gabata, inda na shaidar cewar, mai share hawaye zai bayyana daga Nijeriya a shekarar 2023 wanda zai share yammacin Afurka daga dukkan wani ƙunci na talauci da bauta,” a cewar sa.

“Don haka, bisa ababe da muka koya daga kura-kuren mu na baya da abubuwa da muka fahimta a tattaunawar mu ta haɗin kai, da a baya aka yi masu rashin fahimta da aiwatarwa, don haka ya zame wajibi na ambaci wanda dukkan alamu suka nuna, zai kai mu tudun natsaira.

“Wannan ɗan taliki ba wani ba ne face Sanata Bala Mohammed, Gwamnan jihar Bauchi mai riƙe da ragamar mulki.”

Kwamared Afiyo ya bayyana cewar, wannan ba wai fata ba ce, lamari ne da aka yi yaƙinin sa da ikon Mahalicci, “gaskiyar managa ita ce, Bala Mohammed wani tagomashi ne na musamman wa Nijeriya daga Ubangijin talikai, da zai ciccivo ko ƙwato Nijeriya, da ma ɗaukacin Afurka ta Yamma daga dukkan cukwikwiye ko dabaibayi daga shekara ta 2023.

“Abu ne na ba-za-ta ko zato na fito fili ina bayyana zaɓi na, na shugabancin Nijeriya. Amma gaskiyar lamarin shine, Nijeriya tana cikin wani hali na ba-za-ta wanda yake buƙatar ɗauki da karsashi na ba-za-ta.

“Bugu da ƙari, dillalan sharri sun rigaya sun riƙe dukkan madafun rayuwa a Nijeriya, don haka ƙasar tana buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kan lokaci, haɗi da taimakon ƙasashen waje ya zuwa shekarar 2023, domin tabbatar da samun canji nagari.

“Masu girma dattaijai da abokai na, ina tabbatar maku cewar, Sanata Bala Mohammed yana da karsashin da zai kiyaye da bunƙasa Nijeriya, kuma matuƙar an ba shi jagorancin Nijeriya, zai yi matuƙar tabbatar da ƙarko da zaman lafiyar ta, waɗanda suke wajibai ne na bunƙasa da cigaba.

“Wannan mutum ne wanda ga dukkan alamu ya nuna ƙwarewa, fasaha, gaskiya, adalci, ƙarfin zuciya, jaruntaka, da tawali’u, maras nuna bambancin addini ko ƙabilanci. Ɗumgurungum ma dai, mutum mai kamanta gaskiya da tsoron Allah.

“Mutum ne mai kunnen sauraro, kana ya ɗauki shawarwari da suka jivanci ƙasa, tare da nuna ɗalibancin ɗaukar shawarwari da ake bashi.

“Irin wannan mutum da yake da nagartattun halaye na rayuwa, idan aka damƙa masa jagorancin Nijeriya, za ka kwatanta shine da mutane irin su Sankara, Mboma, Sadauna, Awolowo, Azikiwe da Boros,” a cewar sa.

Ya ƙarƙare da cewar, bai wa Sanata Bala Mohammed goyon baya ya zama shugaban Nijeriya a shekara ta 2023, goyon baya ne wa zaman lafiya, haɗin kai da cigaban ba Nijeriya kaɗai ba, har ma da shiyyar yammacin Afurka baki ɗaya.

Afiyo dai, yana wannan jawabi ne a matsayin sa na babban sakatare na Ƙungiyar Sarakunan Afurka ta Yamma (AWAM), da kuma Jagoran Shugabannin Zaurukan Matasan Arewacin Nijeriya (NYLF) a taron tattaunawa na 17 na zaɓaɓɓun shugabannin gargajiya, dana matasa daga ƙasashe masu magana da harshen turanci na yammacin Afurka, wanda aka gudanar a ranakun 23 zuwa 25 ga watan Fabrairu, 2022 a Otal ɗin ‘Airport View Hotel’, da ke birnin Akara ta Ƙasar Ghana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *