Gwamna Bala ya zama shugaban gwamnonin PDP

Daga BASHIR ISAH

An zaɓi Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, yayin da Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya zama mataimakin shugaban ƙungiyar.

An zaɓi Mohammed da Fubara ne a wajen taron bitar da PDP ta shirya wa zaɓaɓɓun jami’anta wanda ya gudana a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi a ranar Asabar.

Gwamna Mohammed ya maye gurbin gwamnan Oyo ne, wato Seyi Makinde, wanda shi ma ya halarci taron na yini guda.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban riƙo na ƙasa na Jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya nuna wa jagororin buƙatar da ke akwai a haɗa kai a yi aiki tare.

Saboda a cewarsa, sai da haɗin kai za a samu cigaba da kuma ɗaukakar da ake buƙata.

A nasa ɓangaren, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda shi ma ya halarci taron, ya soki matakin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka na cire tallafin mai ba tare da samar da madadinsa ba.