Man fetur, tun ana dariya za a koma kuka!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk ’yan Nijeriya sun san halin da a ke ciki a yanzu na janye tallafin man fetur gaba ɗaya a jawabin da sabon shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi bayan shan rantsuwar shiga ofis. Ba a ko kai sa’a biyu zuwa uku ba a ka fara ganin sakamakon janye tallafin na fetur inda gidajen mai su ka tumbatsa da masu neman mai.

A Abuja wasu gidajen man sun rufe ne ma sai matasa masu jarka a ka riqa gani a ko ina su na sayar da man kan farashi mai tsada. Ashe dai tsadar jarkar ma nafila ce in an duba yadda yanzu farashin ya zama daga Naira 194 a cikin Abuja zuwa Naira 540. Dama wasu jihohin sun kwan biyu a tsadar fetur inda ni kai na a nan Jihar Nasarawa daf da Abuja na sayi lita Naira 350 lokacin da a cikin gari a ke sayarwa Naira 194.

Duk ba tsadar farashin litar ne mafi zama abun damuwa ba yadda hakan a dan ƙanƙanin lokaci zai shafi farashin muhimman kayan masarufi. Labarun da mu ke samu yanzu kuɗin mota musamman tsakanin garuruwa ya ninka da fiye da kashi 100! Idan kuwa sufuri ya zama haka to ai ba ma sai an jira mako ɗaya ko biyu ba za a ga fassarar hakan a kwaryar abinci. Komai na rayuwa kai tsaye ko a kaikaice na alaƙa da farashin fetur.

Shugaba Tinubu a shafinsa na TIWITA ya fito ya na batun ya gaji cire tallafin ne daga gwamnatin Buhari inda ya ce ba a ma tanada kuɗin tallafin a kasafin kuɗi ba don haka zuwa ƙarshen watan nan na Yuni ba ko sisin kobo da za a samu don biyan tallafin. Tuni kuma masu sharhin tattalin arziki musamman da ke aiki da ’yan jari hujja su ka fara kwatanta farashin litar fetur a Nijeriya da sauran sassan duniya kamar Turai da ƙasashen Larabawa da nuna man fetur ɗin Nijeriya na arahar gaske in an duba farashin sauran ƙasashe.

Sun cigaba da cewa matuƙar ba cire tallafin za a yi ba za a wayi gari gwamnati ba ta kuɗin hatta biyan albashi balle ɗaukar nauyin sauran ayyukan raya ƙasa. To in kuwa haka ne sai kowa ya shirya don za a shiga mafi tsannain tsadar rayuwa da rashin samun abinci. Idan gidaje za su wayi gari ba abinci to fitina za ta fara daga nan kenan. In fitina ta fara daga gida za ka ga mutane da a baya ke dariya ta koma yake za su murtuke kuma za a rika samun yawan bacin rai kana bun da bai taka kara ya karya ba.

Lokacin da mutane su ka shiga yanayin fushi da rashin uzuri za a koma tamkar zaman ’yan marina kowa da inda ya fuskanta. Tun da can ina labarin alƙawarin farfaɗo da matatun man fetur na gamnati? Matatar man fetur ta Fatakwal, Warri da Kaduna da ba a maganar aikin su? Ƙasashen da a ke sayo man daga wajen su ta yaya su ka inganta hanyoyin ta ce mai da sayar da shi?

Gaskiya akwai tambayoyi da yawa da shugabannin Nijeriya za su amsa. Nijeriya ta koma dandalin jari hujja ta yadda har dai mutum ya na da kuɗi ba ya tuna cewa sauran miliyoyin mutane na nan ba su da rogon da za su ci. Tsadar nan ta fitar hankali ba za ta dami masu juyawa ko wuƙa da nama ba don iskar da su ke shaqa ma ta daban ce. In haka ne wa zai iya gyara Nijeriya in ba komawa kacokan ga neman taimakon Mahaliccin Sammai da Ƙassai ba.

Sabon shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya hau mulki da karyawa da soke tallafin man fetur.

Wannan ne babbsn abun da Tinubu ya ce ya amince da shi nan take daga abun da gwamnatin Buhari ta gadar ma sa muradin yin hakan da ke tsare.

Shugaban wanda ya sha rantsuwa bisa tanadin tsarin mulki; ya ce tallafin ba shi ds wani amfanin da ya wuce azurta ‘yan jari hujja.

Duk da lalle hakan zai jefa talakawa a karin ƙunci; Tinubu ya raka matakin da cewa za a tura tallafin wani sashen da zai fi taimakon al’umma.

Tinubu ya ce, duk ‘yan Nijeriya na sa ne kuma ya miqa tayi ga sauran ‘yan siyasa su zo a tafi tare.

Kazalika ya ce zai daidaita canjin Naira, samar da tsaro da ba wa mata da matasa dama.

Tun gabanin nan tsohon shugaba Buhari ya yi bankwana ya kama hanyar Daura wasu na juyayi wasu na Allah raka taki gona

Shugaban magoya bayan Tinubu Kailani Muhammad ya ce bai yi wani juyayi ba.

Sheikh Abdullahi Bala Lau na daga mahalarta taron da yin addu’ar haɗin kan Nijeriya.

Hannatu Musawa na daga matan da su ka nuna kwarin gwiwar nasara a sabuwar gwamnatin.

Ko me za a ce yanzu ba za a dorar da manyan bayanai ba sai an ga kamun ludayin naɗa muƙaman gwamnatin Tinubu.

Dogayen layukan neman fetur sun cigaba a gidajen mai a Abuja tungabanin aiyana sabon farashin litar man da a bisa yadda a ka saba daga nan hakan zai shafi farashin muhimman kayan masarufi sai ƙuncin rayuwa ya ƙara ta’azzara.

Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC ta nuna matuƙar damuwa ga yadda Tinubu ya yi saurin sanar da janye tallafin kamar yanda ya gada daga Buhari.

TUC ta buƙaci zama domin duba duk hanyoyin da za su kawo maslaha ga ƙalubalen.

Shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyari ya ce ba zai yiwu a iya biyan tallafin ba don ba tanadin hakan a kasafin kuɗi.

Kamfanin man fetur na Nijeriya ya zayyana gyara fomfon litar man fetur da hakan ya bambanta daga wannan jiha zuwa waccar da ya danganta a bisa ma’ana daga nisa daga bakin teku.

Kakakin kamfanin na NNPP Garbadeen Muhammed ya bayyana cewa an ƙara ko daidaita farashin man bisa haƙiƙanin yadda kasuwa ta ke a yanzu bayan janye dukkan tallafin da gwamnati kan bayar a baya.

Kamfanin ya nuna jajantawa jama’a ga matsalolin da za su fuskanta bisa wannan sabon yanayi ya na mai ba da tabbacin gamsar da abokan hulɗa.

Takardar jerin farashin man fetrur da a ka yayata ta a kafafen labarun yanar gizo na nuna farashin litar man fetur ɗin ta fara daga Naira 488 a Lagos ta kai har mafi tsada a arewa maso gabar kamar Gombe zuwa Naira 550.

Yayin da a babban birnin Nijeriya Abuja farashin litar ta ke Naira 540 ta na zaman Naira 511 a Fatakwal da ke tsakiyar kudu maso kudu.

Hakanan a Sokoto can Arewa maso yamma bayanin ya nuna litar na Naira 540 a Maiduguri jihar Borno ta na mafi tsadar farashi Naira 557.

Cigaba da sanin farashin ya nuna ta na Naira 545 a Birnin Kebbi jihar Kebbi yayin da ta ke Naira 515 a Owerri jihar Imo.

Haƙiƙa fito da farashin ya sanya dogayen layukan mai sun vace a gidajen mai don da alamu mutane ba su da kuɗin saya.

An ga talakawa na rage hanya ta hanyar tafiya da kafa a babban birnin Nijeriya Abuja don rashin ƙarfin aljihu da zai sa su iya biyan kuɗin mota mai tsadar gaske.

Tun farko an ga dogayen layukan mai a safiyar ranar Laraba sun cika gidajen mai amma can da yamma da farashin gaskiya na ɗan karen tsada ya fito sai motoci su ka watse a gidajen mai don rashin kuɗin iya sayan ko da lita biyu ne.

Wasu masu motocin haya kan zuba lita 5 zuwa 10 da a baya bai fi Naira 1000 zuwa 2000 amma yanzu hakan ya haura dubu 500 zuwa 10 da kuma ba ma kuɗin sayan don haka ba amfanin tinkarar fomfon mai balle a ji kunya.

Tun a tarihin Nijeriya ba a taba samun mafi tsadar litar fetur ba sai daga lokacin da gwamnatin Buhari ta hau mulki a 2015 da kuma yanzu a 2023 da Bola Tinubu ya hau karaga a ƙarƙashin jam’iyyar su ta APC da ta kwace ragama bayan mulkin PDP na tsawon shekaru 16.

Lamarin ya fara kamar za a iya samun mako ɗaya ko fiye kafin tsadar ta fara don tunanin man da ke kasa na da tallafin sa amma sai a ka ga saɓanin zaton da a ka yi.

Ta kan yiwu ba wai ’yan kasuwar fetur sun ci bulus ba ne don ba mamaki kamfanin na NNPC ya yi lissafin man da ke a kasa ya zare tallafin sa ya bar ’yan kasuwa su sayarwa talakawa da tsada in ya so su fanshe kuɗin su wajen jama’ar ƙasa.

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago da fadar Aso sun tashi daga taron duba janye tallafin fetur ba tare da cimma matsaya ba.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC Komred Joe Ajaero da na kmafanono TUC Komred Festus Osifo ne su ka jagaoranci tawagar kwadagon zuwa taro a ɗakin taron shugaban ma’aikata na fadar in. Ada bayan tattaunawa Ajaero ya ce sam ba a samu maslaha ba.

Ajaero ya nuna takaicin yanda a na cikin tattaunawar sai kawai kamfanin NNPC ya yi biris da taron da ayyana farashin man fetur “Ai ba daidai ne ka yi amfani da barazanar bakin bindiga wajen sanya abokin tattaunawar ka ya amince da yarjejeniya ala tilas ba” Inji Ajaero da ke tabbatar da cewa ayyana farashin ya jefa jami’an ƙungiyar a mawuyacin yanayi don hakan yankan baya ne.

Bayanai dai sun nuna za a dawo don cigaba da tattaunawar da zummar cimma matsayar da za ta samar da sassauci kenan ga ’yan Nijeriya.

Kammalawa;

A tarihi dai kusan sau daya ne a ka taɓa ƙara farashin fetur a ka kuma zo a ka rage; shi ne zamanin mulkin marigayi Umaru ’Yar’adua da kuma Goodluck Jonathan. Za a rage ko ba za a rage ba ya na da muhimmanci mutane su koma ga neman taimakon Allah ta hanyar duba daga zunubbai da taimakawa masu ƙaramin ƙarfi. Dabarar ɗan adam ba za ta yi amfani da a wannan yanayi.