‘Yan bindiga sun kashe mutum 26 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai wani sabon hari kan manoma a ƙauyukan Jambako, Sakida da Saulawa na Ƙaramar Hukumar Maradun inda suka kashe mutum 25.

Wani ganau ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai hari kan mutanen ƙauyen ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da safiyar Asabar.

Wani mazaunin ƙauyen Sakida mai suna Malam Ɗayyabu ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, an kashe mutum 21 a Jambako, sannan biyar daga Sakida da Saulawa samu raunuka.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun fara kai wa mutanen Sakidda hari ne a gonakinsu, inda wasu ‘yan ƙungiyar ’yan banga daga Jambako suka garzaya don yaƙar su, inda aka rasa mutum 18 sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun binne mutum 21 a garin Jambako da rana, yayin da sauran biyar din ‘yan ƙauyen Sakida aka binne da yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” in ji Malam Dayyabu.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ƙi cewa komai, amma ya yi alƙawarin zai yi tsokaci nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *