Gwamna Buni Ya tabbatar wa sojoji goyon bayan gwamnatinsa

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya karɓi baƙuncin Kwamandan Sojojin Runduna ta biyu, Operation HAƊIN KAI, Birgediya Janar BMG Martins.

A wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun gwamnan Jihar Yobe, Mamman Mohammed, ya ce gwamnan ya bai wa kwamandan tabbacin cewa gwamnatin jihar tare da al’ummar jihar, za su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya don samun nasarar yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Ya ce, “gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin samun dawamamen zaman lafiya mai ɗorewa da tsaro a ko ina a jihar.”

Gwamna Buni ya bayyana gamsuwarsa da Kwamandan, inda ya tabbatar masa da goyon baya dangane da ayyukan sojojin rundunar haɗin kai a jihar.

Da farko, Kwamandan ya jaddada neman buƙatar rundunar wajen ci gaba da goyon bayan al’ummar jihar.

“Mun himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya tare da samun cikakken tsaro a jihar da kuma yankin Arewa maso Gabas baki ɗaya, don mutane su rayu cikin kwanciyar hankali da harkokin su na yau da kullum.” In ji Janar Martins.

A hannu guda kuma, mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam, shi ne ya gabatarwa da gwamnan lambar yabo da aka ba shi sabida gudunmawarsa wajen gina zaman lafiya da ci gaba a Jihar Yobe.

By ukarofi