
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Nasarawa, sun fara gudanar da bincike game da mutuwar yara guda biyar a wata mota da aka daina amfani da ita.
Lamarin ya auku ne a ƙauyen Agyaragu dake Ƙaramar Hukumar Obi a jihar.
A sanarwar da Kakakin rundunar, Ramham Nansel ya fitar, ya ce sun samu rahoton ne a ranar 4 ga watan Mayu, inda wani mai suna Mista Ozimna Ogbor daga ƙauyen ya sanar da jami’ansu.
Ya bayyana sunayen yaran kamar haka; Kamsi Onah mai shekaru 8, Somer Onah ɗan shekara 6, Unice Udouchi ƴar shekara 10, Nmasoma Nnaji ita ma ƴar shekara 10, da kuma Chioma Nnaji mai shekaru 8.
Ya ce, an same su ne a motar dake gidan wani mutum mai suna Mista Abu Agyeme, wanda shi ma ɗan ƙauyen ne.
Jin rahoton ke da wuya, Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Shetima Jauro Muhammad ya umarci jami’ansu na yankin da su gaggauta gudanar da bincike.
A yayin da aka garzaya da yaran zuwa wani asibiti ne, sai likitan da ya karɓe su ya ce akwai yiwuwar sun mutu ne a sakamakon rashin iskar shaƙa.
Daga nan ne kwamishinan ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi akan lamarin, wanda irinsa ya taɓa faruwa a Ƙaramar Hukumar Keffi dake jihar a watan Agustan 2019, inda yara biyu suka rasa rayukansu a wata mota da aka ajiye.
Ya kuma yi kira ga iyaye da ɗaukacin al’umma da su riƙa sanya ido da kula musamman kan al’amuran da ka iya cutar da ƴaƴansu.
